'Za a iya koma wa gidan jiya game da annobar cutar HIV'

Wata ma'aikaciya a dakin gwaji Hakkin mallakar hoto Getty Images

Rikon sakainar kashi da kasashen duniya suke yi wa cutar da ke karya garkuwar jiki ta HIV kan iya sa a sake samun bullar cutar, a cewar wani rahoto.

Kwararru sun yi gargadin cewa tsaikon da aka samu game da tallafin da ake bayarwa wajan yaki da cutar a shekarun baya-baya nan na kawo cikas ga kokarin da ake yi na dakile yaduwar cutar.

Idan aka dubi halin da ake ciki yanzu, zai yi wuya kasashen duniya su iya cimma burinsu na kawo karshen cutar nan da shekarar 2030 - wanda shi ne lokacin da mambobin Majalisar Dinkin Duniya suka amince da shi, a cewar wani bayani da kwarraru suka wallafa a mujallar The Lancet.

Sun yi kira a kan a gudanar da sauye-sauye cikin gaggawa akan matakan da ake dauka wajan bada magani da kuma dakile yaduwar cutar.

'Abubuwa sun tsaya'

Mutane miliyan 37 a fadin duniya ne suke dauke da kwayar cutar HIV ko SIDA. Kuma an yi kiyasin cewa mutane miliyan 1,800 ne suke kamuwa da cutar a kowace shekara.

An shekarun baya-bayanan an samu raguwa a yawan masu kamuwa da cutar HIV/SIDA.

Sai dai mujalar The Lancet ta ce ana fuskantar tafiyar hawainiya a kokarin da ake yi na rage yawan masu kamuwa da cutar zuwa 500,000 nan da 2020 kamar yadda hukumar yaki da cutar HIV take son a cimma.

Sai dai duk da cewa ana samun raguwa a yawan masu kamuwa da cutar HIV a duniya, har yanzu tana tasiri a tsakanin mutanen da ake nuna wa tsangwama, da matasa musamman mata da kuma kasashe masu tasowa, kuma dukaninsu suna cikin rukunin da zai yi wuya su samu maganin rage radadin cutar, in ji mujallar.

Kwararru sun ce an fuskanci koma baya a tallafin da ake bayarwa domin yaki da cutar a shekarun baya-bayanan. Kuma ana bukatar kudi fye da fam biliyan 50 domin cimma muradun hukumar UNAIDS.

Dr Linda-Gail Bekker, wadda ita ce shugabar kungiyar kwararru kan cutar SIDA ta duniya wadda farfesa ce a jamiar Cape Town, ta Afrika ta kudu ta ce: "Duk da cewa an samu nasara sosai a matakan da ake dauka a kan cutar HIV, amma an fuskanci tsaiko a cikin shekaru 10 da suka gabata.

"Farfado da wannan aiki ba karamin abu bane - amma makomar lafiyar miliyoyin mutane ta bukaci mu shawo kan kalubalen."

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mujallar The Lancet ta kuma nemi kwararru a kiwon lafiya a kan su kara hada karfi da karfe wajan yaki da cutar kuma ya kamata a shigar da shirin samar da maganin cutar a wasu fannonin kiwon lafiya.

Wannan na nufin sai an kawo karshen tsarin nan na maida hankali kan cutar HIV ita kadai, inda ake ware kudi tare da gudanar da ayyuka na musaman kan cutar.

Kuma wannan na nufin cewa sai an hada da tsarin yin gwaji kan cutar da kuma cututtukan da ba a kamuwa da su ta hanyar jima'i irinsu ciwon suga da kuma hawan jini.

Misali a Indiya an hada gwajin cutar HIV da gwajin da ake yi wa mata da kuma 'yan luwadi maza da suka kamu da ciwon sanyi, kuma wannan zai rage yawan masu kamuwa da cutar a kasar da kashii bakwai cikin dari daga 2018 zuwa 2028, in ji rahoton.

"Ya kamata a tsara tsarin kiwon lafiya ta yadda zai iya biyan bukatun mutane," in ji Farfesa Chris Beyrer.

"Bai kamata a bar wani a baya ba a kokarin da mu ke yi na samar da tsarin kiwon lafiya mai dorewa ."

Labarai masu alaka

Karin bayani