'Yan takara 28 ne za su fafata da Paul Biya a Kamaru

Paul Biya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Paul Biya ya shafe shekaru kusan 36 yana shugabanci a Kamaru

'Yan takara 28 ne hukumar shirya zabe a Kamaru ta bayyana cewa sun gabatar da takardunsu na neman tsayawa takarar zaben shugaban kasar bana.

Babban zaben wanda za a gudanar a ranar 7 ga watan Oktoba zai kunshi har da Shugaba Paul Biya da ke neman yin tazarce bayan shafe shekara 36 yana mulki a kasar.

Akwai mata guda biyu daga cikin 'yan takarar 28 da suka nuna sha'awar fafatawa da Mista Biya.

Karo na bakwai ke nan da Shugaba Biya mai shekara 36 ke tsayawa takarar zaben shugaban kasa a Kamaru.

'Yan takarar da za su fafata da shugaban sun kunshi 22 daga jam'iyyun siyasa, yayin da shida kuma ma su zaman kansu ne.

Hukumar zabe ta rufe karbar takardun 'yan takara da karfe misalin 12 na dare a ranar Laraba bisa tsarin dokar zaben.

Daga ranar Alhamis ne hukumar shirya zaben a Kamaru ta fara zama domin gudanar da bincike kan sahihancin takardun 'yan takarar zaben na shugaban kasa.

Hukumar zaben za ta wallafa sunayen wadanda suka cancanci tsayawa takara bayan ta kammala aikin tantance su karkashin sharuddan da doka ta shimfida.

Hukumar tana da wa'adin gudanar da aikin zuwa ranar 8 ga watan Agustan bana.

Labarai masu alaka