Yaushe za a kawo karshen auren dole a Najeriya?
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda aka 'aura wa' yarinya mijin da ba ta taba gani ba

Akwai zato mai karfi da mutane suke yi cewa babban aikin iyaye maza shi ne aurar da 'yarsu mace ga namiji mutumin kirki.

Wannan ke janyo iyaye ke yi wa 'ya'yansu mata auren dole ga mazajen da ba su kaunarsu ko ra'ayi.

Wannan al'adar ta karfafa ne saboda yadda mutane suka dauki saba wa iyaye a matsayin babban laifi, kamar yadda addinin Musulunci ya nuna.

A arewacin Najeriya ana yi wa yara mata auren dole fiye da kima.

Wasu daga cikin matan na hakuri su zauna da mazajen, wasu kuma suna yakar wannan dabi'a, kamar wata baiwar Allah da na tattauna da ita a wannan makon.

Adadin auren dolen da ake a arewacin Najeriya yana da yawan gaske.

A addinin Islama, daya daga cikin ginshikai ma su mahimmanci na shari'ar aure shi ne amincewar masu auren domin idan ba su amince ba to babu auren! Amma me ya sa iyaye suke watsi da bukatar 'ya'yansu?

Wasu sukan ce talauci ne ke haddasa auren dole amma ana samun haka har ma a gidajen masu arziki da wadata.

Ina ganin hakan na ci gaba da faruwa ne domin babu wani hukunci mai tsauri da ake dauka game da iyayen da ke yi wa 'ya'yansu auren dole.

Wannan na haifar da matsaloli ga 'yar da ta ki yarda ta bi umarnin iyayenta kan yin auren dole, lamarin da kan kai wasu ga yin karuwanci a garuruwa na kusa da kuma nesa.

Ina fatan shirin Adikon Zamani na wannan makon zai ja hankalinka/ki. Ina fatan zai sa ka hana auren dole a duk inda ka ga za a yi shi.

Da fatan zai zaburar da kai ka goyi baya tare da tallafawa yarinyar da ka ga za a tilasta wa yin auren da babu soyayya a ciki wanda a lokuta da dama kan zamo mai illa a gare ta.

Labarai masu alaka