Zababbun hotunan Afirka a makon da ya gabata

Zababbun hotunan da suka fi kyau daga Afirka da 'yan Afirka a wasu wurare a duniya a wannan makon.

Masoya kwallon kafa a Abidjan na kasar Ivory Coast suna murnar nasarar da Faransa da samu na lashe gasar kofin duniya a Lahadi. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Masoya kwallon kafa a Abidjan na kasar Ivory Coast suna murnar nasarar da Faransa da samu na lashe gasar kofin duniya a Lahadi.
Dan wasan bayan Faransa Presnel Kimpembe yana sunbatar kofin duniya da Faransa ta lashe a Rasha Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nasarar Faransa- 'Yan Afirka na ganin kamar Afirka ce ta lashe kofin duniya a Rasha ganin yawan bakaken fata da suka mamaye tawagar Faransa.
'Yan Kenya rike da tutar Amurka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ranar Litinin 'yan kasar Kenya sun hada gangami inda suka fito gefen titi domin tozali da tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama a lokacin da ya kai ziyara zuwa kauyen mahaifin sa da ke yammacin kasar.
Wani dan kasar Kenya ya yi wa babur din sa ado da hoton Obama domin girmama tsohon shugaban na Amurka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani dan kasar Kenya ya yi wa babur din sa ado da hoton Obama domin girmama tsohon shugaban na Amurka
Wata mabiya addini a Kenya tana cikin wadanda suka fito suna jiran isowar Barack Obama domin bude wani wurin wasanni da motsa jiki. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wata mabiya addini a Kenya tana cikin wadanda suka fito suna jiran isowar Barack Obama domin bude wani wurin wasanni da motsa jiki.
Mista Obama ya shaida wa mutanen da suka halarci wani taron da aka shirya masa a filin kwallon kwando inda ya shaida ma su tasirin wasan a rayuwarsa. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mista Obama ya shaida wa mutanen da suka halarci wani taron da aka shirya masa a filin kwallon kwando inda ya shaida ma su tasirin wasan a rayuwarsa.
Ranar Laraba, dalibai a birnin Durban na Afrika ta kudu sun yi bikin cika shekara 100 da haihuwar marigayi tsohon shugaban Afirka ta kudu Nelson Mandela. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ranar Laraba, dalibai a birnin Durban na Afrika ta kudu sun yi bikin cika shekara 100 da haihuwar marigayi tsohon shugaban Afirka ta kudu Nelson Mandela.
Wani mai basirar zane ya yi amfani da kasa a bakin tekun Puri a India inda ya zana hoton tsohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela a ranar da ake bikin cika shekara 100 da haifuwarsa. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani mai basirar zane ya yi amfani da kasa a bakin tekun Puri a India inda ya zana hoton tsohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela a ranar da ake bikin cika shekara 100 da haifuwarsa.
Manyan 'yan siyasa saman rakuma suna yakin neman zabe a yankin Gao da ke Arewacin Mali Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Manyan 'yan siyasa saman rakuma suna yakin neman zabe a yankin Gao da ke Arewacin Mali
Protesters in Rabat, Morocco - Sunday 15 July 2018 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wasu 'yan Morocco a babban birnin Rabat suna zanga-zangar yin kira ga gwamnati ta saki wadanda aka kama a lokacin zanga-zangar kin jinin gwamnati a a al-Hoceima bara.
Mutane na tafiya cikin ruwa a Aboisso da ke kudu maso gabashin Ivory Coast a ranar Asabar bayan ambaliyar da ruwan sama ya haddasa. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane na tafiya cikin ruwa a Aboisso da ke kudu maso gabashin Ivory Coast a ranar Asabar bayan ambaliyar da ruwan sama ya haddasa.
Wani dan sanda tsaye kusa da wani jirgin kasa da ya yi hatsari bayan ya sauka daga layinsa a birnin Cairo ranar Juma'a. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani dan sanda tsaye kusa da wani jirgin kasa da ya yi hatsari bayan ya sauka daga layinsa a birnin Cairo ranar Juma'a. A
Daga dama wani mawakin Najeriya Seun Kuti da 'yan kungiyarsa suna yin waka a ranar Asabar a wani a wani gidan casu da ke garin Huesca a kasar Spain. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Daga dama wani mawakin Najeriya Seun Kuti da 'yan kungiyarsa suna yin waka a ranar Asabar a wani a wani gidan casu da ke garin Huesca a kasar Spain.

Hakkin mallakar hotuna daga AFP, EPA da kuma Reuters

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC