Gobara ta cinye shaguna a kasuwar Jos

Wata mummunar gobara ta lakume shaguna da runfuna da dama a babbar kasuwar Terminus a garin Jos da ke tsakiyar Najeriya.

Gobarar ta yi sanadiyar hasarar dukiya mai yawa kamar yadda daya daga cikin 'yan kasuwar da gobarar ta shafa ya shaida wa BBC.

"Gobarar ta tashi ne kusan misalin karfe biyu na dare a bangaren da ake kira Baluje a babbar kasuwar ta garin Jos." in ji shi.

Ya ce gobarar ta ci runfunan 'yan kasuwa na wuccin gadi da dama wadanda har yanzu ba su iya kayyade adadinsu ba, sannan kuma ta taba wasu shaguna a kasuwar.

Kuma ya ce har yanzu ba a gano musababin gobarar ba, saboda a cikin tsakiyar dare ne gobarar da ta fara ci.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Undie Adie ya shaidawa manema labarai cewa sun samu labarin gobarar lokacin da ta fara tashi kuma nan take suka sanar da jami'an kashe gobara wadanda suka yi kokarin takaita al'amarin.

Kawo yanzu babu rahotannin hasarar rayuka da aka samu sakamakon gobarar.

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Labarai masu alaka