An kame faston da ya kasa tayar da matacce a Habasha

Faston ya sha kashi bayan ya kasa tayar da gawa Hakkin mallakar hoto Screen Capture/Facebook
Image caption Faston ya sha kashi bayan ya kasa tayar da gawar

An kame wani Fasto da ke da'awar cewa "Annabi ne" bayan ya kasa tayar da gawa a kasar Habasha.

'Yan sanda sun kame faston mai suna Getayawkal Ayele bayan ya kasa tayar da gawar wani mutum da ya mutu kwanaki hudu da suka gabata.

Lamarin ya faru ne a wani gari da ake kira Galilee a Wollegga yammacin Habasha.

Tuni hoton bidiyon faston ya mamaye shafukan sada zumunta inda aka nuna shi a cikin kabari yana kokarin tayar da mataccen.

Bidiyon ya nuna Faston a kwance saman gawar yana kiran sunan mamacin.

Tun da farko Faston ya samu 'yan uwan mamacin mai suna Belay Biftu inda ya ba su labarin yadda Annabi Isa (AS) ya tayar da matacce.

"Na ga mutane da dama suna gudu zuwa kabarin da aka binne mamacin suna cewa Belay zai tashi, na fada wa mutane kada su yarda karya yake yi amma suka kore ni wai ban da imani", kamar yadda wani malamin coci a garin Dhinsa Debela ya shaida wa sashen Oromoo na BBC.

Faston ya sa mutane sun tone kabarin, ya bude mayafin da aka lullube gawar sannan ya fara ihu yana kiran "Beley ka tashi"

Ya dauki lokaci yana kai komo a kabarin, har sai da mutanen da suka taru suna kallo da 'yan uwan mamacin suka hasala suka fara dukan faston kafin 'yan sanda suka zo suka kwace shi.

Rundunar 'yan sandan yankin ta tabbatar wa da BBC cewa Faston yana hannunta.

Cin mutuncin gawa dai babban laifi ne a tsarin dokar kasar Habasha.

Labarai masu alaka

Karin bayani