An dawo da ‘yan Najeriya da suka makale a Rasha

An dawo da 'yan Najeriya da suka makale a Rasha Hakkin mallakar hoto @GeoffreyOnyeama

An dawo da 'Yan Najeriya 155 da suka makale a Rasha bayan kammala gasar cin kofin duniya.

A ranar juma'a da dare ne jirgin da ya kwaso su ya sauka Abuja.

Ministan harakokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama wanda ya tarbe su bayan isowarsu Abuja, ya ce gwamnati ta yi shatar jirgi ne domin dawo da su gida.

Mista Onyeama wanda ya wallafa hotunan isowar 'yan Najeriyar a shafinsa na Twitter ya ce shugaba Buhari ne ya bukaci a gaggauta dawo da su daga Rasha.

'Yan Najeriyar wadanda suka tafi domin domin marawa Super Eagles baya a wasannin gasar cin kofin duniya sun makale ne a Rasha saboda matsalar kudi.

Wasunsu sun tare ne a ofishin jekadancin Najeriya bayan sun makale a Rasha.

Gwamnati Najeriya na zargin kamfanonin da suka yi dillacin tafiya da su ne suka soke tikitin dawo wa da su ba tare da sun sanar da su ba

Ministan ya ce ofishin jekadancin Najeriya ne ya dauki nauyin kula da wurin kwanansu da kuma abinci a Moscow kafin a dawo da su