An fara jigilar mahajjata a Najeriya

Maniyatan Najeriya Hakkin mallakar hoto @nigeriahajjcom
Image caption Maniyatan Kogi 446 suka tashi daga Abuja zuwa birnin Madina a ranar Asabar.

Najeriya ta fara jigilar rukunin farko na maniyata aikin hajji zuwa kasar Saudiyya.

An fara jigilar maniyatan ne daga jihar Kogi, inda kimanin 446 suka tashi daga Abuja zuwa birnin Madina a ranar Asabar.

Jirgin Max air ne ya fara jigilar maniyatan wadanda suka kunshi maza 228 da kuma mata 218, kamar yadda hukumar alhazzai ta kasa NAHCON ta wallafa a shafinta na Twitter.

Ministan Abuja Musa Bello ne ya wakilci shugaba Muhammadu Buhari domin kaddamar da fara aikin jigilar maniyatan zuwa Saudiyya.

Shugaban na Najeriya ya jaddada tabbatar da tsaron alhazzan na Najeriya da kare lafiyarsu a dukkanin kwanakin da za su kwashe suna ibadah a Saudiyya har zuwa dawowarsu.

Daga yanzu za a ci gaba da jigilar maniyatan a sassan jihohin Najeriya zuwa kasar Saudiyya.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, jakadan Najeriya a masallatai ma su tsarki na Makkah da Madina, Adnan Mahmoud Bastaji ya ce an fara jigilar maniyatan ne bayan hukumomin Saudiyya sun sanar da kammala shirye-shiryen karbar maniyata aikin hajji.

"An samar da dukkanin abubuwan da suka dace domin karbar maniyata aikin hajji daga sassan duniya a biranen Madina da kuma Makkah." in ji shi.

Hakkin mallakar hoto NAHCON
Image caption Adadin Mata 218 a Najeriya ne suka fara tashi zuwa Saudiyya
Hakkin mallakar hoto NAHCON
Image caption Yadda aka tantance maniyatan na jihar Kogi a Abuja kafin su tashi zuwa Saudiyya

Labarai masu alaka