Dan sanda ya wanka wa mai jego mari

Dan sandan ya yi kokarin korar matar daga banki Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wani bidiyo da aka yi ta yayata shi a kasar Ghana ya janyo matukar bacin rai tsakanin jama'ar kasar, bayan an ga wani dan-sanda na cin zarafin wata mata da ke shayarwa a wani banki.

Bidiyon ya nuna wani dan-sandan na dukan wata mata goye da jariri.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam da dama ne suka yi Allah-wadai da al'amarin.

Al'amarin na zuwa ne 'yan kwanaki bayan an zargi 'yan-sanda da kashe wasu da ake zargin 'yan fashi ne su bakwai, lamarin da ya harzuka mutane a Kumasi birni na biyu mafi girma a kasar.

Wadannan al'amura sun sake janyo muhawara kan kwarewar aikin 'yan sanda a Ghana.

Matar dai ta shaida wa BBC cewa, dan sandan ya mare ta ne gami da duka a lokacin da ta je cire kudi a banki.

Ta ce, a ranar da taje cirar kudin akwai matsalar na'urar cire kudi wato ATM, hakan ya sa ta zauna ta jira a gyara saboda ba ta da ko sisin da zata sayi abincin da zata ciyar da jaririn nata.

Matara ta ce, a garin jiran ne dan sandan ya ce lallai sai ta bar wajen, ita kuma ta tsaya gardama, to bata an kara ba sai kawai taji saukar mari a fuskarta.

Daga nan kuma sai duka baji ba gani ga kuma goyo a bayanta.

Ta ce ko da ta tambayyi dan sandan cewa ko don jaririn da ke bayanta ba zai raga mata ba, ko kuma idan aka yi wa matarsa haka zai ji dadi? sai ya ce mata babu abinda ya dame shi, aikinsa ya ke.

Labarai masu alaka