An bullo da sabon maganin Malaria

A kowacce shekara zazzabin cizon sauro na sanadin mutuwar dubban mutane Hakkin mallakar hoto Getty Images

Masu lura da harkar magunguna a Amurka sun amince da wani maganin da ake sha lokaci guda, wanda zai iya warkar da zazzabin cutar cizon sauro wato malaria da ya ki jin magani.

Maganin mai lakabin Tafenoquine, shi ne na farko da aka amince da shi a kasar bayan shekara 60, domin amfani da shi wajen warkar da mutane daga na'u'in zazzabin cizon sauro na malaria Vivax.

A yanzu dai magunguna da ake da su na da bukatar a sha ne na tsawon kwana 14 a jere, sai dai mutane da dama kan daina shan maganin da zarar sun samu sauki, abinda ke sanya cutar sake dawowa.

A wani bincike da hukumar lafiya ta duniya WHO ta gudanar, ta ce za a iya kawo karshen zazzabin cizon sauro a cikin 'yan shekaru a kasashe irin Senegal da Gambia da Zimbabwe da Algeriya da Comoros da kuma Madagascar.

A kowacce shekara zazzabin cizon sauro na sanadin mutuwar mutane 4,000, yawancinsu kuma yara kanana ne 'yan kasashen Afirka.

A wasu kasashen Afirka mata masu juna biyu na yawan mutuwa saboda zazzabin cizon sauro, duk kuwa da cewa gwamnati, da 'yan siyasa da kungiyoyi masu zaman kansu, da hukumar lafiya ta duniya na kokarin bai wa mata masu juna biyun tallafin gidan sauro mai magani da kuma allurar riga kafi.

Amma har yanzu ana nuna damuwa, a kan yadda mutane ke ci gaba da mutuwa sakamakon kamuwa da mutane ke yi da zazzabin cizon sauron a kasashe kamar Najeriya da Ivory Coast da Sudan ta Kudu da kuma Jamhuriyar tsakiyar Afirka.

Karanta wasu karin labaran