An yi jana'izar Farfesar da barayi suka kashe a hanyar Abuja-Kaduna

Jana'iza Hakkin mallakar hoto Kaduna Government
Image caption A ranar Litinin ne aka yi jana'izar marigayiyar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna a Najeriya ta ce akalla mutum hudu ne aka kashe a lokacin da wasu barayi suka tare hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Cikin mutanen da aka kashe a harin na ranar Lahadi, har da Tsohuwar Kwamishinar Ilimi ta jihar Katsina Farfesa Halimatu Idris, kamar yadda 'yarta ta tabbatarwa da BBC.

Sai dai rundunar 'yan sandan ba ta bayyana sunaye ko yankunan da wadanda suka mutu suka fito ba.

Ba ya ga mutanen da aka kashe, bayanai sun kuma ce barayin sun yi garkuwa da wasu karin mutane, a harin wanda aka kai tsakanin garin Jere da Katari.

An dade ana garkuwa da jama'a domin neman kudin fansa a hanyar Kaduna zuwa Abuja, abin da yake ci gaba da ciwa matafiya tuwo-akwarya.

'Yan kasar da dama na sukar yadda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke tunkarar lamarin, amma jami'ai sun sha nanata cewa suna iya kokarinsu domin shawo kan matsalar.

Image caption Ana yawan sace wa da kashe mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Diyar marigayiya Farfesa Halimatu, ta shaida wa BBC cewa mahaifiyarta ta tashi ne daga Kaduna zuwa Abuja, babban birnin kasar, a ranar Lahadi.

A wannan hali ne kuma kwararriyar malamar makarantar ta hadu da ajalinta.

"Muna gida aka ce min na tafi Katari, sai na taras da ita a wani asibiti da harbin bindiga, tana tari da korafin cewa tana jin zafi".

Ta kara da cewa "ta shafe dogon lokaci kafin a dauke ta zuwa asibiti saboda rashin motar daukar marasa lafiya, kuma kafin mu kai asibitin Allah ya yi mata cikawa".

A ranar Litinin ne aka yi jana'izar marigayiyar a birnin Kaduna kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i ya wallafa a shafin Twitter cewa "yana aiki tare da gwamnatin tarayya domin kawo karshen sace-sace da fashi da makami a jihar. Ko wanne rai na da matukar muhimmanci:

Masu lura da al'amura na ganin wannan ba karamin rashi ba ne musamman ga fannin ilimin yankin arewacin Najeriya, ganin cewa ba kasafai ake samun mata da suka kai matakin ilimi na Farfesa ba a yankin.

Hakkin mallakar hoto Kaduna government
Image caption Jami'an gwamnatin Kaduna da sauran al'umma dama ne suka halarci jana'izar marigayiyar
Hakkin mallakar hoto Kaduna Government
Image caption Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin siyasa Mallam Uba Sani ne ya wakilici gwamnati a wurin

Labarai masu alaka