Gasar Hikayata: An shiga mataki na gaba

hikayata

An shiga matakin tantance labaran da aka shigar a Gasar Rubutun Kagaggun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, wanda ya kasu kashi biyu.

A matakin farko, za a yi tankade da rairaya a fitar da labarai 60 wadanda suka cika ka'idojin shiga gasar, sannan a sake tacewa a fitar da 25 a kashi na biyu.

Wadannan 25 din ne za a mika ga alkalan gasar, su kuma su fitar da na daya, da na biyu, da na uku.

Da zarar an fitar da labaran 25 kuma za a sanar da wadanda suka rubuta su.

A watan Oktoba ake sa ran bayar da kyaututtukan kudi - dalar Amurka 2,000 ga wacce ta yi ta daya; dalar Amurka 1,000 ga wacce ta yi ta biyu; da kuma dalar Amurka 500 ga wacce ta zo ta uku - da lambobin yabo ga marubuta ukun da za su yi zarra a Gasar.

Da tsakar daren ranar Lahadi ne dai aka rufe kofar karbar labarai a gasar ta Hikayata ta bana.

Saurari wasu labaran Gasar Hikayata ta 2017

Labarai masu alaka