Zan dakatar da ministan Buhari daga APC – Oshiomhole

Oshiomhole Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugaban jam'iyya mai mulki ta APC a Najeriya, Adams Oshiomhole, ya koka kan yadda wasu ministoci a kasar ba sa "bin umarnin jam'iyya", inda har ya yi barazanar korar ministan kwadago Chris Ngige.

Mista Oshiomhole ya fadi hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a fadar shugaban kasar.

A baya-baya nan ne jim kadan bayan zamowarsa shugaban jam'iyyar APC, Mista Oshimhole ya bai wa ministan kwadago da na sufurin jiragen sama Hadi Sirikia umarnin su nada sabbin shugabannin hukumomin da ke karkashin ma'aikatunsu, kamar yadda gwamnati ta amince.

Akwai hukumomi da dama da ke karkashin manyan ma'aikatun gwamnatin tarayya da ba a sauya shugabanninsu ba, tun bayan hawan Shugaba Muhammadu Buhari mulki a shekarar 2015, duk da cewa akwai 'yan jam'iyyar da dama da ke korafin cewa an hana su mukamai.

"A ganina babu dattaku ga duk wani minista da yake zagon kasa ya kuma kasa rike girmansa ta yin abin da bai dace ba, babu wanda ya fi karfin jam'iyya," in ji Mista Oshimhole.

Ya kara da cewa: "Ni a jam'iyya ba zan dauki sakacin da shugaban kasa ke dauka daga wajen masu rike da mukaman gwamnati ba.

"Kuma idan muka kori mutum to za mu gamsar da shugaban kasa cewa wannan mutum bai cancanci zama a majalisar shugaban ba, don ba ya bin umarninsa kuma ba ya yin biyayya ga jam'iyya, wacce ba don ita ba da ba su kai matsayin da suke kai ba a yanzu.

"Na fada na kara nanatawa, babu wani minista da ya fi karfin jam'iyya, kuma suna amfani da yadda shugaban kasa ke nuna dattako wajen kawar da kai kan abubuwa da dama.

Mista Ngige dai ya mayar wa Oshiomhole martani a cikin wata wasika cewa ba zai bi umarninsa ba, umarnin Shugaba Buhari kawai zai bi.

Masharhanta dai na ganin barin tsoffin shugabannin hukumomin wadanda suke tun zamanin Goodluck Jonathan na kawo nakasu ga tafiyar wannan gwamnatin.

Mista Oshimhole dai ya jaddada cewa duk ministan da bai bi umarni da aka ba shi ba, to ba makawa za su tabbatar da cewa an cire shi, yana mai gargadinsu cewa ba zai dauki irin abin da suke yi a baya ba.

"Ko dai su yi biyayya ko kuma mu kore su daga jam'iyya. Idan muka kore su za mu ga yadda gwamnati za ta ci gaba da tafiya da 'yan aware," in ji shugaban jam'iyyar.

Labarai masu alaka