Kun san tarihin farfesar da aka kashe a hanyar Abuja?

Halimatu Sadiyya Idris Hakkin mallakar hoto Twitter/@Shehusani

Ranar Lahadi ne dai wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kama wasu mutane tare da kashe wasu mutum hudu tsakanin garin Jere da Katari a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Cikin mutanen da suka kashe akwai Farfesa Halimatu Sadiyya Idris.

BBC ta samu zantawa da maigidanta, Abdullahi Mu'azu, game rayuwarta, kuma ya bayyana yadda rayuwarta ta kasance kamar haka:

An haifi Halimatu Sadiyya Idris ranar 7 ga watan Yuni na shekarar 1958.

Ta yi karatun sakandare a Queen's College ta jihar Legas da kuma Queen Amina College ta Kaduna.

Daga nan sai ta koma College of Adavnced Studies Zaria (CAST Zaria) inda ta yi karatu tsakanin shekarar 1976 zuwa 1979.

Ta yi karatu a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ta samu digiri a shekarar 1981.

Ta yi wa kasa hidima a Kwalejin Barewa a shekarar 1982.

A shekarar 1983 ta samu aiki a CAST Zaria inda ta koyar zuwa shekarar 1987 da aka samu jihar katsina.

Da aka ware jihar Katsina daga Kaduna, sai ta koma aiki a ma'aikatar ilimin jihar Katsina.

Ta yi shugabancin makarantar sakandaren mata ta GGSS Malumfashi na tsawon shekara biyu kafin ta zama shugabar makarantar 'yan mata ta GGSS Sandamu.

Daga nan ta koma ma'aikatar ilimi ta jihar.

Ta dai yi digiri na biyu da digirin-digirgir a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

A shekarar 1997 ce ta fara koyarwa a jami'ar Abuja inda take aiki har ta rasu.

Sai dai kuma ta yi aiki a matsayin kwamishiniyar ilimi a jihar Katsina tsakanin watan Disambar shekarar 2015 zuwa shekarar 2017.

Ta kasance mace ta farko a jihar Katsina da ta fara zama Farfesa.

Kafin rasuwarta farfesa ce ta ilimin kimiyyar halittu da kuma kwarin da ke cutar da dabbobi (wato biology & vetenery parasitology).

Hakkin mallakar hoto KADUNA GOVERNMENT
Image caption Tuni dai aka yi jna'aizar Halimatu Sadiyya Idris

Labarai masu alaka