An cire haraji a kan audugar mata a India

Akshay Kumar Hakkin mallakar hoto Hindustan Times

Jarumi Akshay Kumar wanda ya fito a cikin fim din Pad Man, fim din da ya yi kokari wajen wayar da kan al'umma a kan muhimmancin tsafta a yayin da mace ki jinin al'ada, ya jinjina wa hukumar da ke zartar da hukunci a kan abubuwan da suka jibanci haraji a Indiya saboda cire wa audugar mata wato Pad haraji.

Akshay Kumar ya zubda hawaye tare da bayyana farin cikinsa a shafinsa na twitter, inda ya ce nagode wa wannan hukuma saboda fahimtar da ta yi na bukatar tsafta a yayin jinin al'ada, da kuma saukakawa mata wajen samun audugar da suke amfani da ita.

Jarumin ya ce ' Na tabbata da yawan mata yanzu za su rinka samun damar amfani da auduga saboda harajin da aka cire mata wanda ya sanya ta yi tsada ta kuma karfin wasunsu'.

Akshay Kumar dai ya yi amfani da kasancewar sa jarumi inda ya fito a cikin wani fim da ya nuna yadda ya yi kokari wajen samar da auduga mai sauki ga mata.

Fim din mai suna Pad Man wanda matarsa Twinkle Khanna ta shirya shi ya samu karbuwa saboda darasin da ya ke dauke da shi.

Pad Man dai, Labari ne na wani mutum da ya shafe shekara 20 yana gwagwarmaya domin ya saya wa matarsa audugar al'ada, amma daga karshe ya kare da taimakawa rayuwar miliyoyin mata a fadin duniya.

Kuma Labarin fim din ya samo asali ne tun a shekarar 1998, lokacin da wani sabon ango wato Muruganantham ya fuskanci amaryarsa Shanti na boye masa wani abu.

Mista Muruganantham, ya ce ba wani abu ba ne illa wani tsumma mai dauda wanda za ta yi amfani da shi a lokacin da take al'ada.

Mista Muruganantham, ya ce ko da goge babur dinsa ba zai iya yi da tsumman da take amfani da shi ba.

Wannan dalili ya sa Mista Muruganantham ya shiga gwagwarmayar samar da wata na'ura mai saukin kudi da za ta iya yin audugar mata da ke kira pad a turance.

A yanzu matan India miliyan 40 na amfani audugar Mista Muruganantham, kuma akwai shirin cewa za a kai irin wadannan na'urorin sarrafa audugar zuwa kasashen Kenya da Najeriya da Sri Lanka da kuma Bangladesh.

Fim din Pad Man da ka sake shi a cikin shekarar da muke ciki ya samu karbuwa matuka gaya, hakan ya ba wa Akshay Kumar damar samun lambobin yabo da dama saboda rawar da ya taka a fim din.

Hakkin mallakar hoto Forbes

Radhika Apte da Sonam Kapoor na daga cikin wadanda suka fito a fim din.

Karanta wasu karin labaran

Labarai masu alaka