Mace ta sake zama shugabar hukumar zabe a Ghana

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo, ya sake nada mace a matsayin sabuwar shugabar hukumar zabe ta kasa.

Matar mai suna Jean Adukwei Mensa, ita ce babbar jami'ar cibiyar gudanar da harkokinn tattalin arziki ta IEA (Institute of Economic Affairs) a kasar.

Jean Adukwei Mensa, Lauya ce da ake yi wa kallon wadda ta taka rawar gani a bangaren kwarewa a nazarin manufofi da shawarwari.

Kazalika an zabe wasu mutane biyu a matsayin mataimakan ta da na ukun su wanda zai maye gurbin wani kwamishinan zaben da ya yi murabus.

Yanzu ana jiran amincewa daga majalisar kasa, wadda tarihi ya nuna koda yaushe suna goyon bayan duk wani nadi na shugaban kasa.

Wannan sanarwa ta zo ne bayan an cire shugabar hukumar zabe Madam Charlotte Osie da mataimakan ta biyu ,

An cire su ne bayan wani bincike zargin cin hanci da rashawa da wani kwamiti ya gabatar, sannan ya bukaci a sallame su daga aiki.

Karanta wasu karin labarin

Labarai masu alaka