Kocin Najeriya ya karbi 'na-goro' don zabar 'yan wasa

Kocin Super Eagles Salisu Yusuf
Image caption Salisu Yusuf ya ce kudin da ya karba ba su sabawa ka'ida ba

Wani hoton bidiyo ya nuna yadda mai horas da 'yan wasan Super Eagles Salisu Yusuf, ya karbi kudi a hannun wasu mutane yayin tattaunawa kan zaben 'yan wasan da za su taka rawa a gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Mutanen sun ba wa kociyan kudi ne yayin da suka nuna masa tamkar wakilai ne na wasu 'yan wasa da ke son a dauke su domin taka rawa a gasar CHAN ta masu taka-leda a cikin gida.

Sai dai Salisu Yusuf, ya shaida wa BBC cewa ba ya tunanin ya karya dokokin hukumar kula da kwallon kafa ta duniya, wadda ta haramta wa jami'anta karbar na-goro.

'Yan jaridar na tare da Anas Armaya'u, wani dan jarida mai binciken kwa-kwaf na kasar Ghana.

Babu tabbas ko kudin da kocin ya karba ya yi tasiri a kansa wajen zabar 'yan wasan.

Tun farko Salisu Yusuf, sai da ya shaida wa 'yan jaridar cewa zabar yan wasan da za su buga a gasar CHAN ana yi ne dangane da kokarin mutum da kuma kasancewar yana buga wasa a koda yaushe.

Sannan kuma ya shaidawa BBC cewa shi dala 750 ya karba, ba dala dubu guda ba, kuma ya yi amanna cewa kudin ba su yadda haramcin karbar na goron FIFA zai shafe shi ba.

Kawo yanzu babu wani martani da ya fito daga Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, NFF, wacce ta samu kanta a cikin wani rikici na shugabanci.

Karanta wasu karin labaran