'Yan sanda sun yi wa 'gidan Saraki kawanya'

Yan sanda Hakkin mallakar hoto Omisore/Twitter
Image caption Tun da sanyin safiya ne 'yan sandan suka mamaye titin gidan Bukola Saraki

'Yan sanda sun tare duka hanyoyin shiga layin da gidan Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki Saraki ya ke a Abuja.

Mataimaki na musamman ga Mr Saraki, Bamikole Omisore, ya wallafa hotunan da ya ce jami'an tsaro ne lokacin da suka tare duka hanyoyin zuwa gidan sanatan, wanda ke unguwar Maitama.

Daya daga cikin masu taimakawa Saraki ya shaida wa BBC cewa tun da sanyin safiya ne 'yan sandan suka mamaye titin Lake Chad inda gidan sanatan ya ke, kuma suka hana shi fita duk da cewa ya shirya tun tuni.

Sai dai daga bisani BBC ta fahimci cewa Mr Saraki ya fice daga gidan saboda ya samu bayanan cewa 'yan sanda za su yunkurin hana shi ficewa.

Bayanai sun nuna cewa Sanata Saraki ya yi niyyra zuwa ofishin 'yan sanda ne domin amsa gayyatar da suka yi masa kan zargin da suka ce wasu 'yan fashi da aka kama a jihar Kwara sun yi, na cewa shi ne mai gidansu.

Mr Saraki, wanda ya musanta zargin, ya ce ya samu bayanan da ke nuna cewa gayyatar tasa na da alaka da yunkurin hana wasu sanatoci da 'yan majalisar wakilai na jam'iyyar APC mai mulki sauya sheka.

Tun da asuba ne kuma 'yan sanda da jami'an EFCC suka killace gidan mataimakin shugaban majalisar dattawan Sanata Ike Ekweremadu da ke unguwar Apo, a Abuja, kamar yadda wani na hannun damarsa ya shaida wa BBC.

Jaridar Daily Trust ta rawaito kakakin rundunar 'yan sandan kasar Jimoh Moshood yana cewa ba shi da masaniya kan batun killace gidan shugaban majalisar da mataimakinsa.

Takun saka

Wannan batu na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zaman 'yan murna tsakanin Sanata Saraki da wasu gaggan 'yan jam'iyyar ta APC da kuma bangaren Shugaba Muhammadu Buhari.

Sun dai zargi shugaban da ci musu zarafi da kuma nuna musu banbanci, lamarin da ya kai ga wasunsu yin bore da kafa na su shugabancin jam'iyyar karkashin jagorancin Alhaji Buba Galadima.

Gwamnati da ma jam'iyyar ta APC ta musanta wadannan zarge-zarge.

A wata sanarwa mai dauke da kakkaunsan martani da ya fitar a daren ranar Litinin jim kadan bayan gayyatar da 'yan sandan suka yi masa, Sanata Saraki ya ce gaggawar da 'yan sandan ke yi kan batun ta nuna cewa suna da wata manufa a kasa.

"An aiko min da takardar gayyata da misalin karfe 08.00 na dare sannan aka nemi na bayyana da misalin karfe 08.00 na safe. Wannan na nuna yadda suke gaggawa domin cimma wani buri na musamman".

Ya kara da cewa "ba a bashi jawabin da mutanen da aka kama suka yi a kansa ba", amma kuma ana neman ya mayar da martani a kai.

"Wannan wani shiri ne na tilasta min tare da abokan siyasa ta mu ci gaba da zama a jam'iyyar da ke cin zarafin 'ya'yanta ba tare da wani dalili ba, inda rashin adalci ya yi katutu, kuma ba a mutunta tsarin mulki. Kuma wannan ba zai yi tasiri ba".

Irin wannan dambarwar siyasa da zargin yin amfani da jami'an tsaro domin muzgunawa 'yan adawa ba sabon abu ba ne a Najeriya, sai dai masu sharhi na ganin ya ci karo da alkawuran da Shugaba Buhari da APC suka yi na kawo sauyi a kasar.

Wadanda suka fice daga APC a kwanan nan

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Jam'iyyar APC ta kauce hanya - Buba Galadima
  • Bangaren Akida da Restoration a jihar Kaduna wadanda ke rigima da Gwamna Nasir el-Rufa'i
  • Suna dai samun goyon bayan Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi
  • Bangaren rAPC na Buba Galadima ya kulla alaka da PDP domin kayar da APC a 2019 - wasu na ganin su ma sun kama hanyar ficewa daga jam'iyyar
  • Sanata Abdul-Azeez Nyako da Dan majalisar Wakilai Rufai Umar daga Adamawa - kamar yadda Daily Trust ta rawaito
  • Hakeem Baba Ahmed - shugaban ma'aikata a ofishin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki
  • Usman Bawa - mataimaki na musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.