Shugaba Buhari ya gana da Kwankwaso

Shugaba Muhammadu Buhari da Rabiu Kwankwaso da Adams Oshiomole da Abubakar Badaru Hakkin mallakar hoto FACEBOOK GOVT
Image caption Shugaba Buhari ya gana da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Abubakar Badaru, da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da kuma shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomole a fadar shugaban kasa.

Rahotanni sun ce ganawar da suka yi a ranar Litinin, wani yunkuri ne na dinke barakar da ke tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC.

An yi amannar cewa sanatan da ke wakiltar jihar Kano a Majalisar dattawan kasar na shirin ficewa daga jam'iyyar APC mai mulki tare da magoya bayansa.

Hakan ya biyo bayan sabanin da sanatan ya samu da gwamnan jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje.

Sanatan da magoya bayansa ba su halarci babban taron jam'iyyar APC da aka yi a kwanakin baya ba.

Wata alama da ta kara nuna cewa sanatan da magoya bayansa na shirin ficewa daga jam'iyyar ta APC.

Sai dai za a iya cewa babu tabbas ko ganawar za ta sa tsohon gwamnan ya sauya shawarar da yake yi ta ficewa daga jam'iyyar APC din.

Hakkin mallakar hoto Facebook govt
Image caption Fadar shugaban kasa
Hakkin mallakar hoto FACEBOOK GOVT
Image caption Fadar shugaban kasa

Labarai masu alaka