Sunayen sanatocin APC da suka koma PDP

Snatoci

A ranar Talata ne sanatocin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya 15 suka sauya sheka, inda 14 suka koma babbar jam'iyyar adawa ta PDP, daya kuma ya koma jam'iyyar ADC.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki ne ya bayyana wasikar da sanatocin suka rubuta inda suka bayyana aniyarsu ta komawa jam'iyyar PDP.

Sanatocin sun hada da Rabi'u Kwankwaso, Shehu Sani, Suleiman Hunkuyi da Isa Hamma Misau da Abdul'aziz Nyako da kuma Dino Melaye.

Ga dai yadda shafin Twitter na majalisar ya lissafa su:

 • Sanata Dino Melaye (Kogi)
 • Sanata Barnabas Gemade (Benue)
 • Sanata Ibrahim Danbaba (Sokoto)
 • Sanata Shaaba Lafiaji (Kwara)
 • Sanata Ubale Shitu (Jigawa)
 • Sanata Rafi'u Ibrahim (Kwara)
 • Sanata Suleiman Hunkuyi (Kaduna)
 • Sanata Isa Misau (Bauchi)
 • Sanata Monsurat Sunmonu (Oyo)
 • Sanata Soji Akanbi
 • Sanata Usman Nafada (Gombe)
 • Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ( Kano)
 • Sanata Suleiman Nazif (Bauchi)
 • Sanata Lanre Tejuosho
 • Sai Sanata Abdulaziz Murtala Nyako (Adamawa) wanda ya koma jam'iyyar ADC.

Labarai masu alaka