PDP ta yi maraba da Kwankwaso da sauran sanatocin APC

pdp Hakkin mallakar hoto Getty Images

Jam'iyyar PDP ta yi maraba da sabbin 'ya'yan da ta samu sakamakon sauyin shekar da aka samu a majalisar dokokin kasar.

A ranar Talata ne 'yan majalisa 15 suka bayyana cewa sun fice daga jam'iyyar APC mai mulki, inda 14 daga ciki suka koma PDP.

Mai magana da yawun PDP Kola Ologbondiyan ya shaida wa BBC cewa suna maraba da bakin nasu.

"Wannan wani babban ci gaba ne ga tafarkin demokuradiyyar Najeriya," a cewarsa.

Ya kara da cewa hakan zai ba su damar tserar da kasar daga manufofin "kama-karya na Shugaba Muhammadu Buhari" da kuma bai wa jama'ar kasar mulki mai inganci.

Wannan sauyi dai ya sa jam'iyyar PDP ta zamo mai rinjaye a majalisar yanzu.

Ba mu ji dadin abin da ya faru ba - APC

A nata martanin, jam'iyyar APC mai mulkin Najeriyar ta ce ba ta ji dadin yadda wasu 'ya'yan nata suka sauya sheka ba.

Mai magana da yawun jam'iyyar Bolaji Abdullahi ya shaida wa BBC cewa sun yi iya kokarinsu domin ganin ba a kai ga wannan mataki ba, amma ba su yi nasara ba.

"Za mu ci gaba da daura damara domin tunkarar abin da zai biyo baya," a cewarsa.

Ya kara da cewa har yanzu mu ke da rinjaye a majalisar wakilai, da kuma yawan gwamnoni.

Da aka tambaye shi kan ko 'yan majalisar za su yi yunkurin tsige Shugaba Buhari, sai ya ce:

"Ba na zaton haka zai yi wu domin abu ne mai wuya. Ko Amurka ma bai taba faruwa ba."

Labarai masu alaka