Jagoran R-APC Buba Galadima ya yi hadarin mota

Hadarin mota Hakkin mallakar hoto Whatsapp gashau
Image caption Hadarin ya faru ne kan hanyar Hadeja zuwa Kano a yammacin ranar Litinin

Jagoran 'yan jam'iyyar APC da suka ware daga uwar jam'iyyar Injiniya Buba Galadima ya yi hadarin mota.

Lamarin ya faru ne kan hanyar Hadeja zuwa Kano a yammacin ranar Litinin.

Wani makusancin jagoran Alhaji Sabo Imamu Gashau wanda suke tare a cikin motar lokacin da lamarin ya faru ya ce ba bu wani da ya ji mumunan rauni bayan aukuwar hadarin.

Har ila yau ya ce an sallame su duka bayan garzayawa da su wani asibiti.

Alhaji Sabo wanda shi ne babban mataimaki na musamman na shugaban jami'yyar R-APC ya ce lamarin ya faru ne lokacin da suke kan hanyarsu ta koma wa Kano daga jihar Yobe.

Ya ce motar ta kubuce daga hannun direban ta ne lokacin da ya yi kokarin kauce wa wani mutum da ke kan babur.

Ana yawan samun hadarin mota a Najeriya saboda rashin hanyoyin masu kyau da kuma tukin ganganci.

Labarai masu alaka