Yadda kocin Najeriya Salisu Yusuf ya karbi kudi
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalli yadda kocin Najeriya Salisu Yusuf ‘ya karbi na-goro’

An dauki bidiyon kocin Najeriya Salisu Yusuf yana karbar kudi a boye daga mutanen da suka yi badda kama a matsayin wakilan 'yan kwallo.

Dan jaridar nan na Ghana Anas Aremeyaw Anas ne ya dauki bidiyon a watan Satumbar shekarar 2017 - san nan shirin BBC Africa Eye ya watsa shi a karon farko.

Kocin na Super Eagles, kuma mataimaki na farko yayin gasar cin kofin duniya, shi ne zai jagoranci tawagar kasar zuwa Gasar Olympics a shekarar 2020.