Hoton da ya haifar da rudani a duniyar kwallon kafa

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Daukar hoto wani abu ne na yau da kullum a wurin shahararrun 'yan wasa, sai dai akwai lokutan da hoto guda daya kan iya janyo suka da kuma doguwar muhawara.

Shahararren dan wasan kwallon kafa na Jamus da Arsenal Mesut Ozil, ya yi ritaya daga buga wa kasarsa kwallo bayan sukar da ya rinka sha sanadiyyar daukar hoto da shugaban Turkiyya Racep Tayyib Erdogan.

Iyayen Ozil dai 'yan asalin Turkiyya ne, sai dai shi dan kasar Jamus ne.

An haife shi kuma ya girma sannan ya yi karatu duk a Jamus.

Ozil ya gana da shugaban kasar Turkiyya a watan Mayu, domin a cewar sa " Ya kamata na girmama mutum mafi girman mukami a kasar iyayena".

Sai dai hoton ya dora ayar tambaya a kan biyayyar Ozil ga manufofi na siyasar Jamus.

Shi dai Erdogan ya kori ma'aikata da dama na gwamnati da bangaren shari'a da sojoji da kuma 'yan sanda, bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Wani abu da gwamnatin Jamus ba ta yi maraba da shi ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Daga cikin wadanda suka soki Ozil game da hoton da ya dauka da shugaban na Turkiyya, har da hukumar kwallon kafa ta Jamus (DFB), wadda ta ce " Harkar wasan kwallon kafa da hukumar DFB sun yi hannun riga da Mr Erdogan kan wasu kudurori".

Rashin tabuka abin kirki da Jamus ta yi a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da aka yi a Rasha, ya kara janyo wa Ozil suka a tsakanin masoya kwallon kafa na kasar ta Jamus.

Wannan rikici dai ya haifar da tambayoyi kan tasirin haduwar 'yan wasa da 'yan siyasa.

Sannan kuma ko daukaR hoto da wani dan siyasa na nufin kana goyon bayansa.

Labarai masu alaka