BH: Red Cross 'ba ta shiga tsakani' don ceto mutane

Abubakar Shekau
Bayanan hoto,

Abubakar Shekau ya ce kungiyarsa ba za ta yi sulhu da kowa ba

Kungiyar bayar da agaji ta duniya the International Committee of the Red Cross (ICRC) ta ce ba ta shiga tsakani wurin ceto mutanen da masu tayar da kayar baya irin su Boko Haram suka sace.

ICRC ta bayyana haka ne domin yin raddi kan rahotannin baya bayan nan da ke cewa tana taka rawa wajen ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, musamman a arewa maso gabashin Najeriya.

Wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar Aleksandra Matijevic Mosimann ta fitar ta ce "a matsayinmu na masu bayar da agaji wadanda ba sa nuna bangaranci, ba ma shiga tsakani wurin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su."

"Amma a shirye muke mu dauki mutanen da kungiyoyin masu tayar da kayar baya suka saka domin kai su gidajensu, idan aka bukaci mu yi hakan", in ji sanarwar.

Asalin hoton, Twitter/ICRC_Africa

Bayanan hoto,

Kungiyar agaji ta ICRC ce ta kai wasu 'yan matan Chibok gida

A watan Mayun 2017, kungiyar ICRC ce ta kai wasu 'yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sako gida.

Ta yi hakan ne bayan musayar da gwamnatin Najeriya ta yi, inda Boko Haram ta saki 'yan matan Chibok 82, yayin da ita kuma ta mika wa kungiyar wasu dakarunta da ake tsare da su.

Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya duk da ikirarin da gwamnatin kasar ta sha yi cewa ta fatattake su.