Gwamnan Benue Samuel Ortom ya koma PDP

Ortom

Asalin hoton, Getty Images

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya sanar da ficewarsa daga jam'iyya mai mulki ta APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Mai magana da yawun gwamnan Mr Terver Akase ya tabbatarwa BBC cewa gwamnan ya sauya shekar ne tare da wadansu shugabannin kananan hukumomin jihar 14.

Gwamnan ya sanar da ficewar ne lokacin da ake gudanar da wani taro na shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a birnin Makurdi ranar Laraba, bayan wadansu matasa sun hana shi tafiya Abuja don halartar wani taron sulhun na jam'iyyar APC.

Mista Akase ya ce "ba a yi wa gwamnan abin da ya dace a APC ba. Jam'iyyar ba ta bukatar mutanen Benue, wannan ya sa wadansu matasa a safiyar Laraba suka tare masa hanya a kan hanyarsa ta zuwa Abuja don ganawa da shugaban jam'iyyar APC."

Ya kara da cewa : "Daga nan ne, sai matasan suka bukace shi da ya koma, kuma ba sa bukatar ya ci gaba da kasancewa a jam'iyyar APC."

Sai dai ya musanta cewa gwamnan ya sauya shekar ne saboda zargin da ake masa na gaza kawo karshen kashe-kashen da yake faruwa a jihar.

A ranar Talata ne majalisar dokoki ta jihar ta tsige shugaban majalisar Mista Terkimbi Ikyange wanda dan jam'iyyar APC ne.

Wadanda suka fice daga APC a kwanan nan

Bayanan sauti

Jam'iyyar APC ta kauce hanya - Buba Galadima

  • 'Yan majalisar dokoki ta kasa 52 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP
  • Bangaren Akida da Restoration a jihar Kaduna wadanda ke rigima da Gwamna Nasir el-Rufa'i
  • Suna dai samun goyon bayan Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi
  • Bangaren rAPC na Buba Galadima ya kulla alaka da PDP domin kayar da APC a 2019 - wasu na ganin su ma sun kama hanyar ficewa daga jam'iyyar
  • Sanata Abdul-Azeez Nyako da Dan majalisar Wakilai Rufai Umar daga Adamawa - kamar yadda Daily Trust ta rawaito
  • Hakeem Baba Ahmed - shugaban ma'aikata a ofishin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki
  • Usman Bawa - mataimaki na musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.