Kwalli mai 'gubar dalma' ya yi wa yara illa a Australia

Kwalin Hashmi Kohl Aswad Hakkin mallakar hoto NSW GOVERNMENT
Image caption Hukumomi sun gano gubar dalma a mai yawan gaske a cikin kwalin

Wasu yara uku a Australia sun kamu da rashin lafiya bayan da suka yi amfani da kwalli mai gubar dalma, a cewar hukumomi.

Gwamnatin jihar The New South Wales ta fitar da sanarwar domin ankarar da jama'a a kan kayan kwalliyar na kamfanin Hashmi da ake yi a Pakistan.

An gano cewa akwai kashi 84 na gubar dalma a cikin kayan kwalliyar kamfanin Hashmi da kuma sauran sinadirai masu guba.

Gwamnatin jihar ta ce an shigo da kayayyakin ne ta halattacciyar hanya amma suna kunshe da wasu abubuwa masu hadari.

Likitoci sun ce sun gano gubar dalma a cikin jinin yaran, kuma dukkaninsu 'yan uwan juna ne.

"Binciken da aka yi ya nuna cewa watakila kwallin Hashmi ne ya hadassa rashin lafiyar," in ji Matt Kean, ministan ma'aikatar sa ido kan ayyukan kiwon lafiya.

A baya wasu kasashen duniya sun yi gargadi kan illar da ke tattare da kwallin Hashmi. An haramta sayar da kayan a Amurka.

'Sakon da bai dace ba'

An rika sayar da kayan kwalliyar Hashmi Kohl Aswad da Hashmi Surmi a shagunan da ake sayar da kayan Indiya da Pakistan a birnin Sydney, in ji hukumomi.

"Wasu daga cikin kwalayen kwallin na dauke da sakon da ke cewa babu gubar dalma a ciki, kuma wannan ba dai dai ba ne," in ji Mr Kean.

An dai shawarci 'yan kasar a kan su daina amfani da kayayyakin.

Jami'an tsaron kan iyaka za su sake nazari a kan batun.

Hakkin mallakar hoto NSW GOVERNMENT
Image caption A kasar Pakistan ne ake hada kayan kwalliya na Hashmi

Bayan gubar dalma, kayan kwalliyar na kunshe da sinadarin Arsenic da Cadmium da Chromium da kuma Mercury, a cewar hukumomi.

Ko da gubar dalma kadan ce mutum ya shaka, to wannan na yi wa kwakwalkwa da koda illa.

A zamanin da an rika amfani da dalma a cikin kayan kwalliya ciki har da kwalli - wanda ake amfani da shi a kasashen duniya da dama.

Za a ci tarar duk wani kamfanin da ya sabawa ka'idojin kiwon lafiya miliyan 1.1 in ji gwamnatin jihar New South Wales.

Labarai masu alaka