'An cinna wa masallaci wuta' a Afirka ta Kudu

Masallacin Masjid-e-Mukhtar

Asalin hoton, @wicks_jeff

Bayanan hoto,

An sha kai hari masallatai a Afirka Ta Kudu

An wayi gari wani masallaci na ci da wuta a birnin Durban na Afirka ta Kudu, inda ake zargin wasu ne suka cinna wutar.

An yi nasarar kashe wutar kuma tuni 'yan sanda suka isa masallacin da ake kira Masjid-e-Mukhtar a unguwar Croftdene a Durban.

Limamin masallacin Saleem Adam, ya shaidawa kafar Times Lives ta Afrika Ta Kudu cewa mutanen da suka fara isa masallacin sun tsinkayi wasu mutane uku sun tsallaka katanga suna kokarin tserewa.

Wani ma'aikacin Jaridar Times Live ya wallafa hoton masallacin da ya ci wuta.

Zuwa yanzu ba a tantance dalilin kona masallacin ba.

An dai sha kai hare-hare a masallatai a Afirka ta Kudu.

An taba kashe mutum daya a watan Mayu a wani hari da aka kai da wuka a wani masallaci a Verulum da ke nisan kilomita 30 a arewacin Durban.

A watan Yuni ma an taba kashe mutum biyu a wani hari da aka kai da wuka a wani masallaci da ke kusa da birnin Cape Town.