Mun yi mamakin komawar Ortom PDP – APC

APC

Asalin hoton, Reuters

Jam'iyyar APC ta ce ta yi mamakin sauya shekar Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom daga jam'iyyar zuwa PDP.

A ranar Laraba ne gwamnan ya sanar sauya shekar tare da wasu shugabannin kananan hukumomin jihar 14.

A sanarwar da kakakin APC, Bolaji Abdullahi ya fitar, jam'iyyar ta ce gwamnan ya fice ne a yayin da shugabanta Kwamred Adams Oshiomhole ke kan kokarin magance wasu matsalolin da gwamnan ya gabatar da suka shafi siyasar jihar Benue.

APC ta ce ta yi mamakin ficewar gwamnan bayan ya nuna cewa ya gamsu bayan tabbacin da shugaban jam'iyyar ya ba shi a ganawar da suka yi kan kokarin shawo kan matsalolin.

Gwamna Ortom ya sanar da ficewa daga APC ne lokacin da ake gudanar da wani taro na shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a birnin Makurdi ranar Laraba, bayan wadansu matasa sun hana shi tafiya Abuja don halartar wani taron sulhun na jam'iyyar APC.

Mai magana da yawun gwamnan Mr Terver Akase wanda ya tabbatarwa da BBC ficewar gwamnan daga APC, inda ya ce "ba a yi wa gwamnan abin da ya dace a APC ba."

Sauya shekar gwamnan na zuwa bayan 'yan majalisar dokoki ta kasa 52 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a ranar Talata.

APC ta ce za ta ci gaba da kokarin tattaunawa ta hanyar lallashi domin ganin 'ya'yanta da suka fice sun sauya ra'ayinsu sun dawo jam'iyyar.

Wadanda suka fice daga APC a kwanan nan

Bayanan sauti

Jam'iyyar APC ta kauce hanya - Buba Galadima

  • 'Yan majalisar dokoki ta kasa 52 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP
  • Bangaren Akida da Restoration a jihar Kaduna wadanda ke rigima da Gwamna Nasir el-Rufa'i
  • Suna dai samun goyon bayan Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi
  • Bangaren rAPC na Buba Galadima ya kulla alaka da PDP domin kayar da APC a 2019 - wasu na ganin su ma sun kama hanyar ficewa daga jam'iyyar
  • Sanata Abdul-Azeez Nyako da Dan majalisar Wakilai Rufai Umar daga Adamawa - kamar yadda Daily Trust ta rawaito
  • Hakeem Baba Ahmed - shugaban ma'aikata a ofishin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki
  • Usman Bawa - mataimaki na musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.