Mutum 31 sun mutu a harin da aka kai rumfar zabe a Pakistan

Jamian tsaron Pakistan na bincike a wurin da dan kurnar bakin wake ya kai hari a wata rumfar zabe da ke Quetta

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Kungiyar IS ta dauki alhakin kai hari a Quetta

An kai wa Pakistan hare-hare a ranar farko na zaben shugaban kasar da aka yi - inda mutum a kalla 31 suka hallaka.

Wani dan harin kurnar bakin wake ya tayar da bam din da ke jikinsa a wajen rumfar zabe da ke garin Quetta. Kungiyar IS ta dauki alhakin kai harin.

A wasu wuraren kuma, an samu fashewar abubuwa da barkewar yamutsi inda aka raunata gomman mutane tare da hallaka mutum biyu.

Miliyoyin mutane sun kada kuri'unsu, inda jam'iyyun tsohon dan wasan kurket Imran Khan da tsohon Firai ministan kasar Nawaz Sharif na fafatawa da juna.

An rufe rumfunan zabe da misalin karfe shida na yamma (13:00 GMT), kuma ana kyautata zaton cewa sai a ranar Alhamis ne za a bayanna sakamakon zaben.

An rika nuna damuwa kan magudin zabe da barkewar tashe-tashen hankula a lokacin zaben.

Hukumar kare hakkin bil'adama ta kasar ta ce an rika "kokarin" sauya sakamakon zabe.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Mr Khan ya sha alwashin yaki da cin hanci da rashawa sai dai 'yan hammaya na zarginsa da kasancewar dan amshin shatan sojin kasar, wadanda suka dade suna mulki a kasar.

Mr Sharif, wanda ya yi nasara a zaben bayan an yanke masa hukuncin dauri a gidan kaso bayan badakalar takardun kwarmata bayanai na Panama.

Yaya girman tashin hankalin yake?

Duk da cewa an tsaurara matakan tsaro inda aka girka dubban sojoji da jami'an 'yan sanda a sassa daban-daban na kasar, amma an samu barkewar tashe-tashen hankula.

Bayan harin da aka kai a Quetta da ke lardin Balochistan, mutum daya ya hallaka a harin gurneti da aka kai a Khuzdar, kuma wani ya mutu a harbin bindiga da aka yi tsakanin 'yan hamayya a lardin Swabi, da Khyber da kuma Pakhtunkhwa.

Jaridar The Dawn newspaper ta yi rahoto kan tashe-tashen hankulan da suka faru a Mardan, da Rajanpur, da Khipro da kuma Kohistan.

Wani hari da IS ta yi ikirarin kai wa a wani yakin neman zabe a farkon watan nan kusa da Mastung ya hallaka mutum a kalla 149.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wata mata tana kada kuri'a a rumfar zabe da ke Islamabad