Sauya sheka: Buhari ya gana da 'yan Majalisa

Shugaba Muhammadu Buhari tare da wasu wakilan majalisar dattijan kasarsa

Asalin hoton, Femi Adesina

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi wata ganawar sirri da 'yan majalisar dattawan kasar na jam'iyyarsa ta APC a cikin daren ranar Laraba.

Hakan na zuwa ne bayan ficewar wasu daga 'ya'yan jam'iyyar a majalisar dattijai da ta wakilan kasar.

Ana ganin dai wannan tattaunawa ce mai matukar muhimmancin gaske ganin yadda jam'iyyar ke kan siradi na rasa rinjayenta a majalisar dattijan kasar.

Sanata Shehu Sani, na daga cikin wakilan majalisar da suka halarci ganawar wadda aka yi a fadar shugaban kasar da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ya kuma shaida wa BBC cewa, sun tattauna muhimman batutuwa da dama.

Shehu Sani, ya ce, daga cikin abinda suka tattauna, har da batun halin da jam'iyyar su ta APC ke ciki a majalisun kasar biyu.

Abu na biyu kuma da suka tattauna tare da shugaban kasar shi ne, rikice-rikicen da suka jawo har wasu daga cikin 'yan majalisar suka fice.

Sanatan ya ce, bayan sun tattauna a kan wadannan batutuwan, shugaban Muhammadu Buhari ya yi musu alkawarin zai yi iya bakin kokarinsa ya kawo karshen matsalolin da jam'iyyarsu ke fuskanta.

Kazalika shugaba Buharin, ya kuma yi bayanin cewa, mafi yawancin sanatocin da suke da matsala da jam'iyyar ta su, rikice-rikice ne na jihohi ya haddasa hakan, don haka ya yi alkawarin cewa zai shiga tsakani don kawo karshensa.

Shehu Sani, ya ce daga bisani sun hada kai tare da shugaban kasar inda suka kawo wani kuduri cewa yakamata a ci gaba da hada kan jam'iyyar don a samu nasarar zabe mai zuwa.

Sannan kuma duk wani hukunci da jam'iyyar ta zana, to dole ne kowanne zababban gwamna ko dan majalisa ya yarda da shi inji sanatan.

Karin bayani

A ranar Talatar da ta wuce ne sanatocin jam'iyyar APC mai mulki 14 suka sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP, yayin da wasu daga cikin 'yan majalisar wakilai kuma daga bisani suka bi sahunsu.

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ce ba ta ji dadin yadda wasu 'yayanta suka sauya sheka ba.

Wannan ya sa jam'iyyar PDP ta yi maraba da sabbin 'ya'yan da ta samu sakamakon sauyin shekar da aka samu a majalisun dokokin kasar.

A kwanakin baya ne jam'iyyar APC ta rabu gida biyu inda wasu 'ya'yanta suka kafa nasu shugabancin karkashin jagorancin Buba Galadima.

Sun kira kansu R APC ko kuma gangariyar APC.

Karanta wasu karin labaran