'Rikicin manoma da makiyaya zai iya shafar zaben 2019'

Wani makiyayi na kiwon shanu

Asalin hoton, Getty Images

Wani sabon rahoto ya nuna cewa an rasa rayukan mutane fiye da 1, 300, yayin da wasu mutum dubu 300 kuma suka muhallansu a cikin shekarar nan kadai a rikicin tsakanin manoma da makiyaya a yankin tsakiyar Najeriya.

Wata kungiya mai suna The International Crisis Group, ta ce rikicin zai iya shafar zabukan kasar da za a yi a shekara mai zuwa.

Kungiyar ta ce zai yi wahala ace an wuce kwana guda ba tare da samun rahoto na rikici tsakanin manoma da makiyaya ba a Najeriyar, sai dai yana da wuya a tantance sahihan bayanai na asarar da ake yi.

kungiyar ta ce rikicin ya samo asali ne daga wasu manyan matsaloli da suka hada da sauyin yanayi da karin bukatuwar filin noma.

Amma ta ce rikicin ya ta'azzara ne a 2018. saboda yawaitar kungiyoyin kabilu masu dauke da makamai.

Sannan kuma ta dora alhaki a kan gwamnati na rashin hukunta masu laifi, da bullo da dokar hana kiwo wadda makiyaya ke adawa da ita.

Rahoton ya kuma yi gargadin cewa rikicin ya rikide zuwa na kabilanci da addini saboda mafi yawancin makiyayan musulmai ne kuma fulani, yayin da su kuma manoman yawanci kiristoci ne daga bangaren kabilu daban-daban na kasar.

Karanta wasu karin labaran