An kashe mutum 20 suna sallah a Zamfara

Zamfara

Wasu 'yan bindiga sun kashe mutum akalla mutum 20 a wani hari da suka kai wani masallaci a jihar Zamfara.

Maharan sun bude wuta ne a kan jama'a lokacin da suke sallar La'asar a garin Kwaddi na Karamar Hukumar Zurmi a ranar Talata.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar DSP Muhammad Shehu ya tabbatar da kai harin ga BBC san nan ya ce sun samu gawarwakin mutum hudu.

Wannan shi ne hari na baya-bayan nan da aka kai a jihar, wacce ke fama da hare-haren 'yan bindiga da masu satar shanu.

A karshen makon da ya wuce ma an kashe mutum 31 a wasu kauyuka na Karamar Hukumar Birnin Magaji a jihar Zamfara.

Rahotanni sun ce maharan sun farma garin ne bayan da mazauna kauyen suka gaza hada musu naira miliyan daya kamar yadda suka bukata.

'Yan bindigar sun nemi kudin ne a matsayin "na kariya" kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Irin salo na baya-bayan nan da maharan suka fito da shi na kara jefa mazauna wannan yanki cikin rudani, lamarin da ya sa wasunsu da dama yin kaura daga kauyukansu.

Jama'ar yankin na sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Abdul'aziz Yari da kasa shawo kan matsalar.

Sai dai gwamnatin ta nace cewa tana yin iya kokarinta domin ganin ta kawo karshen lamarin, wanda ya fara haurawa zuwa makwabtan jihohi irinsu Sokoto.

Har ila yau wannan al'amari na zuwa bayan kisan mutane fiye da 50 a cikin mako daya a Zamfara, inda aka kashe mutum 23 a kauyen Zaloka a karamar hukumar Anka da kuma mutum 27 da aka kashe a yankin Gidan Goga da ke karamar hukumar mulki ta Maradun.

Daruruwan mutane aka kashe a jihar a tsawon shekara shida da aka kwashe ana fama da matsalar tsaro a jihar.

Yawaitar kashe-kashen da ake samu kusan a kullum ya tursasawa daruruwan mutanen Zamfara yin kaura zuwa makwabtan jihohi.

Labarai masu alaka