Za mu iya 'lalata komai' na Trump - Kwamandan Iran

Major-General Qassem Soleimani (hagu ), da Donald Trump (dama ) Hakkin mallakar hoto Getty/Reuters
Image caption Janar Qassem ya ce Trump na amfani da harshen 'yan tasha

Wani babban kwamandan zaratan sojojin Iran ya gargadi shugaba Trump kan barazanar Amurka na kai wa kasarsa hari yana mai cewa "za su iya lalata duk abubuwan da ya mallaka".

Kamfanin dillacin labaran Iran na Tasnim ya ambato manjo janar Qassem Soleimani yana shan alwashin cewa idan Trump ya kaddamar da yaki, to Iran za ta ga bayan Amurka.

Hakan ya biyo bayan sakwannin da Mr Trump ya rika tura wa a Twitter inda ya gargadi shugaban Iran kan "kada ya sake yi wa" Amurka barazana.

Zaman doya da manja ya karu tsakanin kasashen biyu tun bayan da Amurka ta janye daga yarjejeniyar nukliya ta shekarar 2015.

Janarar Soleimani - wanda shi ne jagoran askarawan juyin juya hali na kasar ya ce: "A matsayina na soja, mayar da martani ga duk wata barazana, hakki ne da ya rataya a wuyana.

"Ka yi magana da ni, ba shugaban kasa ba (Hassan Rouhani), shugaban kasarmu ba zai mayar maka da martani ba saboda mutunci mukaminsa."

"Muna kusa da kai fiye da yadda kake tunani. Idan ka taba mu a shirye muke."

"Idan ka fara yaki, to mu ne za mu kawo karshen yakin. Ka san wannan yakin zai lalata duk abubuwan da ka mallaka," in ji kwamandan na Iran.

Ya kuma zargi shugaban Amurka da amfani da harshen "yan tasha."

A ranar Lahadi ne, shugabaTrump ya wallafa sako a shafin Twitter yana yi wa shugaban Iran barazana.

Sai dai bayan kwana biyu, a lokacin da yake magana da kungiyar mazan jiya Trump ya ce Amurka "a shirye ta ke ta cimma matsaya" da Iran.

Mista Trump na mayar da martani ne cikin fushi ga wani gargadin da Rouhani ya yi wa Amurka.

Rauhani ya ce "Ya kamata Amurka ta san cewa zaman lafiya da Iran shi ne zaman lafiya da ya fi komi, kuma yaki da Iran shi ne yakin da fi kowanne," kamar yadda kamfanin dilancin labarai Irna ya ruwaito.

A watan Mayun da ya gabata ne, Mista Trump ya yi shellar cewa Amurka za ta janye daga yarjejeniyar nukliyar da kasar ta cimma da Iran karkashin gwamnatin Obama, duk da cewa kasashen turai ba su amince da haka ba.

Mista Trump ya ce "akwai kurakurai "a cikin yarjejeniyar da aka cimma da Iran."

Sai dai Iran ta mayar da martani kan cewa ta soma shirye shiryen inganta shirinta na Uranuim, wanda muhimin abu ne da ake bukata wajen samar da makamshi da makamai.

Gwamnatin Amurka ta sake kakabawa Iran takunkumi kan man fetur da karafa da kuma wasu bangarori duk da cewa Birtaniya da Faransa da China da Jamus sun nuna rashin amincewarsu a kai, kasashen da suka kulla yarjejeniyar 2015 da Iran.

Labarai masu alaka