Kun san su wane ne 'yan Hakika?

Hakika Hakkin mallakar hoto Getty Images

Garin Ngurore da ke karamar hukumar Yola ta kudu bai wuce tazarar kilomita talatin ba daga birnin Yola, hedikwatar jihar Adamawa a arewacin Najeriya.

Duk da cewa sanannen gari ne ta fuskar kasuwanci, a baya-bayan nan ya kara shahara sakamakon bullar mabiya wata akida da ake mata lakabi da "`yan hakika."

Wani bayanin sirrin da ya fito daga hannun rundunar sojin Najeriya da ke Gwoza da ke shiyyar arewa-maso-gabashin kasar, wanda aka kwarmata a kafafen sadarwa na zamani ya nuna cewa an samu bullar `yan hakika ne a garin Ngurore da kuma Toto da ke jihar Nasarawa, dukkaninsu a arewacin Najeriya.

Bayanin sirrin, wanda aka fitar tun a watan Yunin da ya wuce ya yi zargin cewa shan azumin watan Ramadan da barin salloli biyar da kuma yin zina duka ba laifi ba ne a wurin mabiya akidar hakika.

Shin su wane ne `yan hakika?

BBC ta gudanar da bincike ta hanyar ziyartar wadannan garuruwa biyu don tattaunawa da mabiya wannan akida ta hakika.

Mafi yawan ma su wannan akidar dai a boye suke yi sakamakon matakan da mahukunta da shugabannin al`umma ke dauka a kansu.

Saboda haka ba kasafai suke fita fili su tatttauna da bakuwar fuska a kan manufar wannan akidar tasu ba.

Amma duk da haka, BBC ta yi katarin tattaunawa da wani dan kungiyar a garin Ngurore, wanda ya nemi a sakaya sunansa, wanda ke cewa "Hakika tana da dadi ga wanda ya fahimce ta."

A cewar sa, ba haka kawai suke barin sallah ko azumi ko kuma tara wa da mata ba, sai an bi wani mataki da ke ba wa mabiyi damar yin hakan, wanda aka fi sani da tarbiyatul askaru.

Ya ce "duk mutumin da aka ce ya yi tarbiyatul askaru zai fahimci kan sa, ya san wane ne Allah. Kuma idan ka yi nisa za ka shafe komai, ka daina ganin laifin komai."

Ya jaddada cewa isa wannan matakin yana samar da sauki wajen aikata ibada, kasancewar yin wadannan shika-shikan addinin musuluncin ba wajibi ba ne.

Mabiya akidar hakikar suna da ra`ayin cewa ba kowa ne zai fahimci koyarwar akidar ba sai wanda yake cikin kungiyar.

Sun kuma tsaya kai da fata cewa su `yan darikar Tijjaniya ne, wadanda ke tutiya da Sheikh Ibrahim Inyas.

Ana dai zargin cewa wani mai suna Abdullahi, wanda mazaunin garin Numan ne shi ne ya kai akidar hakika garin Ngurore.

Image caption Sarkin Toto Onah Alhaji Muhammadu Umar Azaki

BBC ta yi kokarin bin diddigin shugabanni da mabiya akidar hakika a Numan, amma bayanan da ke fitowa daga garin na cewa wasu daga cikin shugabannin sun yi bulaguro, yayin da wasu kuma ke cewa sun buya, kasancewar jami`an tsaro na farautar su.

A garin Toto na jihar Nasarawa ma, sabanin bayanin sirrin jami`an tsaro da ke cewa`yan hakika sun bulla a garin karkashin jagorancin Yahaya Abdullahi, bayanan da aka samu a garin na cin karo da juna.

Yayin da wasu mutanen garin ke cewa sun ga ma su wannan akidar da idanunsu, shugabannin al'umma kuma na cewa sun gudanar da bincike amma ba su tabbatar da wanzuwarsu a garin ba.

Sarkin Toto, Onah Alhaji Muhammadu Umar Azaki, wanda wazirin Toto ya yi magana da BBC a madadinsa ya ce "an gayyaci shi wannan mai suna Yahaya Ibrahim da wadansu da muke tunanin ba su kula da sallah, mun yi musu tambayoyi daya-bayan-daya ba wanda ya amince ya san da wannan kungiyar."

Siffofin `yan hakika

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Barin salloli biyar da azumi da zina duka ba laifi ba ne a wurin mabiya Hakika

Wasu mazauna Ngurore sun shaida wa BBC cewa galibinsu matasa ne, wadanda ba su wuce shekara 15-30 ba.

Mazajensu kan tara gashi mai yawa a kai, sannan suna rike katon carbi da suke nadewa a hannunsu a matsayin ado.

Suna son cudanya ta maza da mata.

Hakika ba Tijjaniyya ba ce

Wanzuwar `yan hakika ta tada hankalin al`umar Ngurore, sakamakon wasu sabbin dabi`u ko halayen da suka ce `yan kungiyar sun fara nunawa a garin, tare da ikirarin cewa su cikakkun `yan darikar Tijjaniyya ne.

Lamarin ya fara jan hankalin jama`a ne bayan wata yarinya ta bata, kamar yadda wani jagoran Tijjaniyya a garin, Mallam Khalil Sheikh Modibbo Sambo ya shaida wa BBC.

Ya ce "akwai wani magidanci da `yarsa ta bata, sai aka ce tana hannun wasu yara da ake kira `yan hakika. Da muka bincika muka kama su, sannan muka danka su ga hannun `yan sanda."

Malamin ya yi tir da wannan dabi`a ta hakika, yana cewa ba koyarwar Tijjaniyya ba ce.

Dangane da ikirarin da `yan hakika ke yi cewa ta hanyar tarbiyatul askar za a iya shafe laifi ga wanda ya sha azumi ko ya bar sallah kuwa, jagoran Tijjaniyyar ya ce "duk wani askar din da ke kwadaita barin sallah, to kafirci ne."

Irin sukar da malaman addinin musulunci ke yi ga akidar hakika, da kuma farautar mabiyanta da jami`an tsaro ke yi sun sa galibin mabiyanta sun koma suna gudanar da harkokinsu a boye.

Mabiya akidar na kukan cewa ana tauye musu hakkinsu, tun da kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowane dan kasa damar yin addinin da ya kwanta ma sa a rai.

Ni ban dan hakika ba ne- Yahaya Ibrahim

BBC ta samu ganawa da Yahaya Ibrahim, mutumin da jami`an tsaron Najeriya suka yi zargin cewa shi ne shugaban `yan hakika a garin Toto na jihar Nasarawa.

Mallam Yahaya Ibrahim ya musanta wannan zargin, yana cewa "ba ni da makarantar da nake koyar da yara, sannan ba na jagorantar wani masallaci ballantana na yi wa`azi a wajen, kana babu wani faifai da aka taba nadar maganata a matsayin wa`azi," in ji shi.

Ya kuma ya kalubalanci jami`an tsaro idan suna da wata hujjja sai su kafa.

Mallam Yahaya dai ya ce shi dan boko ne, kuma magini, yana jaddada cewa shi mabiyin darikar Tijjaniyya ne tsantsa.

Abin da ya sa hakika ke jan hankalin matasa

Malaman addinin musulunci da dama na ganin cewa sassaucin da ke tattare da akidar hakika ta fuskar hukunce-hukuncen shari`ah shi ne babban dalilin da ke jan hankalin matasa suna rungumar akidar.

Mallam Aminu Yakubu, shi ne baban limamin masallacin juma`a na kungiyar Izala da ke Numan a jihar Adamawa, wanda ke cewa "babban dalili shi ne jahilci, kasancewar galibin wadanda ke wannan akida ba su da alaka da ilimi ta ko`ina, sannan ire-iren wadannan akidu akwai holewa, tun da za a bar mutum ya dinga aikata abin da yake so."

Hakika barazana ce ga tsaro

Shi kuwa shahararren malamin addinin musulunci da ke Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa tsokaci ya yi a kan rikicin da akidar hakika za ta iya haifarwa a tsakanin al`umar musulmi.

A cewarsa "sallolin nan guda biyar an yi ijima`i a yi su, wani ya zo ya ce sallar ma ba sai an yi ta ba. To, ka ga wannan yana iya kawo barazana a harkar tsaro a kasa."

Sheikh Daurawa ya ce "wadansu na iya tashi su afka wa masu irin wannan akidar, wanda zai kai ga iya samun rikicin addini na cikin gida."

`Yan hakika ba ma su tada husuma ba ne

Image caption Tijjaniya ta nesanta kanta da Hakika

Sai dai jami`an tsaro a nasu bangaren sun ce ba za su taba bari `yan hakikar su kai ga zama alakakai ba.

Rundunar `yan sandan jihar Adamawa ta ce ta samu labarin `yan hakikar, amma ta fahimci cewa ba masu son tada zaune tsaye ba ne.

Sufurtanda Usman Abubakar shi ne Kakakin rundunar `yan sandan jihar Adamawa, wanda a tattaunawarsa da BBC ya ce zuwa yanzu dai babu wanda suka kama."

Ya ce 'yan Hakikar ba abin da suke yi da ke jawo fitina. Ra`ayi ne kawai suke nunawa ba dabi`ar fito-na-fito da za ta sa a kama su ba.

Sai dai kuma kakakin 'yan sandan ya ce jami`ansu na farin-kaya suna sa-ido a kan su.

A Najeriya dai ba wannan ne karon farko da mabiya akidar hakika suka bulla a kasar ba.

Ko a shekara ta 2015, sun bulla a birnin Kano, inda hukuma ta daure wasu daga ciki, yayin da wasu kuma suka tuba.

Sai dai bayyanar da mabiya wannan akida suka yi a jihohin Adamawa da Nasarawa da wasu sassan Najeriya da ake zargin ana yada ta a boye, alama ce da ke nuna cewa bakon da aka raka ya dawo.

Kuma a cewar masana, da wuya a yi nasarar dakile ta, har sai an samu cikakken hadin kan sauran mabiya dariku da akidoji daban-daban da ke kasar, ta yadda idan hukuma ta yi hukunci, wani bangare ba zai ce ana yin kage ko saka wa mutanensa karan-tsana ba!

Labarai masu alaka