Hotunan kusufin wata daga sassan duniya daban-daban

Mutane sun sha kallo a kasashen duniya daban-daban yayin da kusufin watan mafi tsawo a karni na 21 ya bayyana.

The Moon rises behind the Temple of Poseidon in Cape Sounion, near Athens Hakkin mallakar hoto Reuters

A kasar Girka ana iya ganin watan a bayan wani wurin bauta na Poseidon da ke Cape Sounion kusa da birnin Athens.

A kusufin wata, duniya ce ke shiga tsakanin watan da Rana.

A "blood moon" rises during a lunar eclipse over Cairo, 27 July 2018 Hakkin mallakar hoto Reuters

Duk da yake rana ba ta haska wata kai tsaye, amma watan na samun hasken rana da ya ke bi ta cikin sararin samaniyar duniyarmu wanda ke karkatar da hasken. Wannan ne dalilin da launin watan ke sauyawa zuwa ruwan lemu, ko ruwan kasa har ma ya kan koma ja gaba daya.

An ga kusufin watan daga Afirka, zuwa Gabas ta Tsakiya da Rasha da kuma Ostreliya.

Clouds over Ely Cathedral in Cambridgeshire obscuring a view of the blood moon Hakkin mallakar hoto PA

Amma ba kowa ne yayi sa'ar ganin kusufin watan ba. Kasar Ingila na fuskantar wani matsanancin zafi a 'yan makwannin nan, amma a wasu yankunan masu bibiyar kusufin sun hallara amma ba su taki sa'a ba, domin yanayi mai kama da hadari ya lullube ko ina.

The blood moon rises behind the Saentis (2502m) Alpstein, Canton of Appenzell, Switzerland, Hakkin mallakar hoto EPA

A yankin tsaunukan Swiss Alps kuwa, mutane sun ga kusufin watan mai launin jini tar-tar.

Star gazers in Sinpapore Hakkin mallakar hoto Reuters

Ba a bukatar sanya tabarau ko wani gilashi na musamman domin kallon kusufin watan.

rises behind the Sheikh Zayed Grand Mosque in Abu Dhabi Hakkin mallakar hoto Reuters

Kusufin watan ya ratsa ta birnin Abu Dhabi, wau sun kalli watan daga babban masallacin Sheikh Zayed.

A full moon is seen near a picture of Brazilian footballer Neymar, before the start of a lunar eclipse over Cairo, Egypt 17 July Hakkin mallakar hoto Reuters

A birnin Cairo kuwa, kusufin watan ya dusar da hasken wata tauraruwa, kamar yadda ake iya gani a saman wani allon talla da ke dauke da hoton dan wasan kwallo na kasar Brazil Neymar.

People set up telescopes to witness a rare lunar eclipse near 27 in Taipei, Taiwan Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mutane da dama sun fita domin kallon kusufin watan a birnin Taipei na kasar Taiwan. Kusufin na yau ya dauki tsawon kimanin sa'a daya da minti 43.

Dukkan hotunan na da hakkin mallaka a kansu.

Karin bayani