Tsoron Buhari ya sa ake fita daga APC - El Rufa'i
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tsoron Buhari ya sa ake fita daga APC - El Rufa'i

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ya ce wasu na ficewa ne daga jam'iyyar APC saboda tsoron wa'adin mulkin shugaba Buhari na biyu.

El-Rufa'i wanda na hannun dama ne ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya fadi wasu dalilai guda uku zuwa hudu da ya ce su ne suka sa wasu 'ya'yan jam'iyyar APC ke ficewa daga Jam'iyyar.

Gwamnan ya ce wasu na ganin shugaba Buhari kwanto ya yi a wa'adin mulkinsa na farko bai kakkama duk barayi ba.

"Kadan ya kama amma suna ganin a wa'adinsa na biyu zai koma ne ya sa kakin soja ya kama dukkanin barayin dukiyar gwamnati ya kulle su."

"Suna jin tsoro idan aka bar shi ya kai wa'adi na biyu ga abin da zai ma su." In ji El-Rufa'i yayin wata ganawa ta musamman da kafafen yada labarai a jihar Kaduna.

Labarai masu alaka