An tura sojoji 1,000 Zamfara don 'yaki da barayin shanu'

sojoji Hakkin mallakar hoto Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta aike sojoji 1,000 jihar Zamfara da ke arewacin kasar don magance matsalar tsaro da barayin shanu da 'yan fashi ke addabar garuruwa da kauyukanta.

A wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce an tura sojoji, da 'yan sanda da sojin sama don su yi aikin hadin gwiwa na tabbatar da tsaro a jihar.

Dakarun sun hada da jami'an sojin kasa da na 'yan sanda da kuma jami'an rundunar tsaro ta farin kaya wato Civil Defence.

Sai dai ba wannan ne karon farko da gwamnatin kasar za ta aike da dakaru yankin ba.

A watan Afrilun da ya wuce ma rundunar sojin saman kasar ta ce ta aike da dakaru na musamman Gusau, bayan da wadansu mahara suka kaddamar da hare-hare a kauyukan karamar hukumar Anka.

Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari ya ce jiragen yaki su ma za su shiga aikin, inda za su dinga gudanar da shi daga filin jirgin sama na jihar Katsina, wadda ita ce mafi kusa da jihar Zamfara don yin wannan gagarumin aikin, bayan sojojin sun shawo kan matsalar rashin man fetur a yankin don gudanar da aikinsu.

A dan tsakanin nan dai jihar Zamfara na cikin wani yanayi maras kyawu, saboda karuwar sace-sacen mutane, da kisan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a iyakar jihar da Kaduna da ke fuskantar matsalar satar mutanen.

Adadin yawan mutanen da ke gudun hijira dai na ci gaba da karuwa a jihar Zamfara sakamakon hare-haren 'yan bindiga da suka addabi kauyukan jihar.

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce a kalla mutum 18,000 suka kauracewa muhallansu sakamakon sabbin hare-haren 'yan bindiga.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Dosara ya shaidawa BBC cewa kauyuka kusan 20 ne jama'arsu suka yi kaura a karamar hukumar Zurmi kadai.

Ya ce mutanen sun watse a kauyukan na mazabu uku wato Mashema da Birane da kuma kwashabawa a karamar hukumar mulki ta Zurmi.

Mutanen kauyukan suna yin kaura ne zuwa cikin garin Zurmi, wasunsu suna asibitin MDG, wasu kuma suna rayuwa ne a makarantun boko na firamare.

Kuma ana gudun hijira ne sakamakon wasikun barazana da 'yan fashi ke aika wa mutanen kauyukan na Zamfara.

Karin bayani game da Zamfara:

  • Kashi 67.5 ke rayuwa cikin talauci
  • Iya karatu da rubutu: Kashi 54.7
  • Take: Noma tushen arzikinmu
  • Yawancin mutanen jihar manoma ne daga Hausa Fulani
  • Yawan jama'a: Miliyan hudu da rabi (Alkalumman shekarar 2016)
  • Musulmi ne mafi yawa
  • Jihar da aka fara kaddamar da Shari'a - a 2000
  • Madogara: Shafin alkalumma na Najeriya da wasu

Labarai masu alaka