Hotunan yadda aka kalli kusufin wata mafi tsawo a duniya

Mutane a kasashe da dama sun ga yadda kusufin wata da ake kira "blood moon" a Turance ya kasance, wanda shi ne kusufi mafi tsawo da aka taba yi a karni na 21.

The Moon rises behind the Temple of Poseidon in Cape Sounion, near Athens Hakkin mallakar hoto Reuters

A kasar Girka, watan ya bayyana ta bayan Wajen Ibada na Poseidon a Cape Sounion, kusa da birnin Athens.

A yayin Kusufin Wata, Duniyar Earth kan kasance tsakanin tauraruwarta da kuma rana.

A picture shows the full moon during a 'blood moon' eclipse beside a statue of ancient Greek god Ares in central Athens on July 27, 2018 Hakkin mallakar hoto Getty Images

Duk da cewa hasken rana ba ya shafar Watan kai tsaye, hasken sararin samaniya yana ratsa Watan. Hakan ke bai wa Watan kalolin ruwan goro da ruwan kasa da kuma ja.

An ga wannan kusufi a Afirka da Gabas Ta Tsakiya da Turai da Rasha da Indiya da kuma Australiya.

A 'blood moon' eclipse is pictured with a sculpture by the American artist Jonathan Borofsky 'Woman walking to the sky' on July 27, 2018 in Strasbourg, eastern France. Hakkin mallakar hoto Getty Images

A birnin Strasbourg na Faransa, an ga Watan ya dusashe ta saman wani mutum-mutumin da wani Ba'amurke Jonathan Borofsky ya yi.

The blood moon rises behind the Saentis (2502m) Alpstein, Canton of Appenzell, Switzerland, Hakkin mallakar hoto EPA

A tsaunukan kasar Switzerland kuwa an ga cikakken kusufin ne.

Star gazers in Singapore Hakkin mallakar hoto Reuters

Ba a bukatar wani tabarau don kallon kusufin.

rises behind the Sheikh Zayed Grand Mosque in Abu Dhabi Hakkin mallakar hoto Reuters

A yayin da watan ya wuce ta Birnin Abu Dhabi kuwa, an gan shi yana wucewa ta hasumayar Masallacin Sheikh Zayed.

The moon is seen turning red over the Sydney skyline during a total lunar eclipse on July 28, 2018 in Sydney, Australia. Hakkin mallakar hoto Getty Images

A Birnin Sydney mutane sun taru don kallon Watan wanda ya zama ja a sararin samaniya.

People set up telescopes to witness a rare lunar eclipse near 27 in Taipei, Taiwan Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mutane a Birnin Taipei na Taiwan, sun yi ta kallon kusufin ta na'urar telescopes. Kusufin ya shafe sa'a daya da minti 43.

A picture of the blood man taken in Dubai, UAE, shows red-tinged clouds across a bright orange moon Hakkin mallakar hoto David Greer
A picture taken in Cairo's Al-Azhar Park shows a bird silhouetted against a golden moon Hakkin mallakar hoto Emad Karim
A picture sent by Emad Karim in Cairo, Egypt shows a glowing orange moon above reddish Egyptian sands Hakkin mallakar hoto Emad Karim

Dukkan hotonan suna da hakkin mallaka.

Labarai masu alaka