Yarinyar da ta kuduri aniyyar kare hakkin Fulani

Yarinyar da ta kuduri aniyyar kare hakkin Fulani

Ba kasafai ake samun 'yayan Fulani makiyaya da sha'awar karatun boko mai zurfi ba, to amma da alama Maryam Sa'idu Baso ta fita daban.

Mairo, kamar yadda ake kiranta a rugarsu ta Nyama da ke garin Akwuke a jihar Enugu, daya ce daga cikin 'ya'yan Ardo Sa'didu Baso, sarkin Fulanin kudu maso gabashin Najeriya da kudu maso kudanci.

Mahaifinsu yana da sha'awar 'ya'yansa da ma sauran 'yayan Fulani su yi karatun zamani, sai dai ba duka ne suke yi ba, don haka yake karfafawa Maryam gwiwar karatun, da kuma daukar dawainiyar karatunta, saboda sha'awar da take nunawa.

A yanzu haka Maryam ta kammala karamar sakandare, tana kuma shirin tafiya babbar sakandare.

Bayanan hoto,

Maryam ta yi karatu ne a wannan aji, kuma a yanzu tana taimakawa kannenta wajen koyar da su karatu da rubutu a rugar Nyama

Babban burinta shi ne ta yi karatu mai zurfi har zuwa jami'a. Tana fatan zama lauya.

"Abin da ya sa na ke son zama lauya shi ne mutanenmu suna samun matsala, saboda babu wanda ya yi karatu ya yi ilimi yake da wani abu. Saboda haka, in na yi lauya zan iya taimakawa mutanenmu a bangaren shari'a."

Ba Maryam ce kadai ke da wannan buri ba, akwai 'yan uwanta a rugar Nyama da ke da irin wannan fata.

Maryam tana rayuwarta ne gaba daya a jihar Enugu da e kudu maso gabashin Najeriya tun daga haihuwa har kawo yanzu.

Hakan ya ba ta damar iya harshen Igbo da ake magana da shi a shiyyar.

Ba ma magana kawai ba, Maryam da 'yan uwanta suna wakokin gada da harshen Igbo, kasancewa suna haduwa wajen wasannin, musamman a makaranta.

To sai dai duk da kasancewa Maryam tana zaune tana kuma karatu a kasar Igbo, ba ta manta yarenta na asali ba wato Fulatanci.

Tana magana da Fulatanci sosai, har ma da rera wakokin harshen.

Watakila hakan dai ba ya rasa nasaba da yadda suke kebe a rugarsu su kadai, da kuma yadda iyayensu suke musu magana da harshen Fulatanci zalla.

Rayuwar Fulani a rugar Nyama dai kusan irinta ake yi a sauran rugage da dama.

An shafe shekaru da dama ana yunkurin kafa makarantun 'ya'yan Fulani domin bunkasa karatunsu.

To sai dai har yanzu makarantun ba su bunkasa ba kamar yadda aka yi fata.

Akwai dalilai da dama da suka hana makarantun bunkasa, abin da kuma ya sa da dama daga 'ya'yan Fulani makiyaya ba su yi karatun zamani ba.

Rashin zaman Fulanin waje guda na daga manyan dalilan da ke kawowa karatun 'ya'yansu koma baya.

Fulani makiyaya na yawan yawo ne suna neman wuraren danyar ciyawa da dabbobinsu za su ci, da kuma inda ruwa yake.

Wani dalilin kuma shi ne rashin malamai a makarantun.

Alal misali a rugar Nyama malami daya ne yake karantar da duka daliban makarantar rugar shekaru da dama.

Akwai kuma karancin kayan aiki, da rashin ajujuwan karatu.

To amma da yake a yanzu Fulanin makiyaya na fuskantar wasu matsaloli fiye da baya, wasunsu sun fara tunanin cewa ya kamata su tsaya su yi ilimin zamani.

Wasunsu na fatan cewa hakan zai saukaka musu wahalhalun da suke ciki da tsangwama da suke fuskanta.

Sai dai duk da haka akwai matasan Fulani da dama da babu abin da suke sha'awa a rayuwa kamar kiwo da suka taso suka ga ana yi.

Bayanan hoto,

A wannan ruga Maryam take rayuwa da iyayenta da 'yan uwanta