Buhari zai gana da limamin da ya boye Kiristoci 262 a Filato

Di Imam wey something cover im face.

Limamin Malam Abdullahi Abubakar nan da sashen Turancin Buroka na BBC ya bayar da labarin yadda ya ceto ran mutane daga mahara zai gana da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

A ranar Litinin ne dai Shugaba Muhammadu Buhari ya gayyaci limamin da ya ceci ran mutane da ke tserewa daga wasu maharan da ake zargin makiyaya ne a Barkin Ladi da ke jihar Filato a tsakiyar Najeriya.

An gayyace shi ne domin ya je ya karbi lambar yabo ta kasar da kuma ganawa da shugaban kasar.

Malam Abdullahi, mai shekara 83 wanda limami ne a kauyen Nghar da ke gundumar Gashish a Barkin Ladi ya boye mutum 262 cikin masallaci da gidansa a ranar 24 ga watan Yuni, na shekarar 2018.

Wadansu mahara ne suka je Barkin Ladi lamarin da ya sa mutane kauyen suka tsere.

Wadanda ya kubutar din sun haida wa BBC cewa sun ji dadin cewa gwamnati na son karrama shi.

Sun ce abin da ya yi abin kwaikwayo ne na gari kuma da ba don shi ba da babu su.

A kwanakin baya ne dai jakadan Amurka a Najeriya ya gana da limamin da kuma shugabannin kauyen Nghar.

Gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya yi shelar cewa shugaban kasar na son ganin limamin a wani taron zaman lafiya da tsaro.

Gwamnan ya ce limamin ya ceci rayuwar Najeriya ce gaba daya ne domin mutum 300 na da yawo.