Cibiyar rukiyya da ake karya mutane a Somaliya

Cibiyar rukiyya da ake karya mutane a Somaliya

Latsa hootn da ke sama don kallon bidiyon:

Binciken kwaf na karkashin kasa da BBC Afirka ke yi ya gano yadda ake amfani da rukiya ta hanyar da ba ta dace ba a Somaliya, makwabciyar Kenya.

Sai dai wani wakilin BBC Somali Jamal Osman ya gano wata cibiya irin wannan da ake cin zarafi da dukan mutane ake kuma tursasa su shan wani ruwa da ake kira harmala.

Sai dai mamallakin cibiyar ta Darushifa ya yi watsi da zargin inda ya ce mutane ke kawo 'yan uwansu cibiyar, wasu kuma da kansu suke zuwa.

Ya kara da cewa suna gyara halayyar masu shan kwaya ne kawai, amma ba sa azabtar da mutane.