Saraki ya koma PDP

Saraki

Asalin hoton, Facebook/Bukola Saraki

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki ya bayyana komawarsa jam'iyyar hamayya ta PDP daga jam'iyya mai mulki a kasar, APC.

Shugaban ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter ranar Talata.

"Ina sanar da 'yan Najeriya cewa bayan tattaunawa, na yanke shawarar fita daga jam'iyyar APC," in ji shi.

Hakazalika Gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmed shi ma ya bayyana fitarsa daga jam'iyyar, kuma ya ce ya koma jam'iyyar adawa ta PDP.

Saraki da Gwamna Abdulfatah wadanda tsofaffin 'yan jam'iyyar PDP ne, sun koma jam'iyyar APC ne a shekarar 2014.

A makon jiya ne Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom shi ma ya sanar da ficewarsa daga jam'iyya mai mulki ta APC zuwa jam'iyyar PDP.

A farkon watan ne Kotun Kolin kasar ta wanke Saraki kan zargin karya wajen bayyana kadarorinsa.

Wadanda suka fice daga APC a kwanan nan

Bayanan sauti

Jam'iyyar APC ta kauce hanya - Buba Galadima

  • Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom
  • 'Yan majalisar dokoki ta kasa 52 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP
  • Bangaren Akida da Restoration a jihar Kaduna wadanda ke rigima da Gwamna Nasir el-Rufa'i
  • Suna dai samun goyon bayan Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi
  • Bangaren rAPC na Buba Galadima ya kulla alaka da PDP domin kayar da APC a 2019 - wasu na ganin su ma sun kama hanyar ficewa daga jam'iyyar
  • Sanata Abdul-Azeez Nyako da Dan majalisar Wakilai Rufai Umar daga Adamawa - kamar yadda Daily Trust ta rawaito
  • Hakeem Baba Ahmed - shugaban ma'aikata a ofishin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki
  • Usman Bawa - mataimaki na musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.