Kotu ta wanke tsohon Gwamnan jihar Sakkwato Attahiru Bafarawa

Bafarawa

Asalin hoton, Twitter/EFFC

Bayanan hoto,

Bafarawa ya kasance gwamnan jihar Sakkwato ne a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007

Wata babbar kotu a jihar Sakkwato ta wanke tsohon Gwamnan jihar Attahiru Bafarawa daga tuhumar karkata kudi da karbar kudin sata da sauransu.

Mai shari'a Bello Abbas ya wanke dan siyarar tare da wadansu mutane hudu daga dukkan tuhume-tuhume da Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya (EFCC) take musu.

Hukumar ta wallafa labarin wanke dan siyasar ne a shafinta na Twitter a ranar Talata.

Alkalin kotun ya ce mai gabatar da kara bai nuna kwararan shaidu da suke tabbatar da tuhume-tuhumen da ake musu ba.

"Babu kwararan hujjoji da za su tabbatar da cewa mutanen sun aikata laifukan da ake tuhumarsu," in ji shi.

Sai dai hukumar EFCC ta ce ba ta gamsu da hukuncin ba, kuma za ta daukaka kara, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter.

An dai fara sauraren wannan shari'ar ce a watan Disambar shekarar 2009.