Kotu ta wanke 'yan shi'a fiye da 80

Wasu mago bayan shia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kotun ta yi watsi da tuhumar da ake yi wa wasu yan shia fiye da 80

Wata babbar kotu a Kaduna, ta yi watsi da tuhumar da ake yi ma wasu 'yan Shi'a fiye da 80 bisa zargin su da hannu a tashin hankalin da ya faru shekaru uku da suka gabata a garin Zariya.

Kotun ta ce gwamnati ta kasa gabatar da kwararan shaidun da za su sa a ci gaba da shari'ar.

Masu gabatar da kara sun tuhumi mutane da kai hari kan jerin gwanon motoccin babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Laftanar janar Tukur Buratai a watan Disemban shekarar 2015.

Sai dai mabiya shi'a sun sha musanta zargin.

Tuni dai mabiya mazhabar shi'a suka fara bayyana fairin cikinsu game da hukuncin kotun.

Mai magana da yawun Kungiyar ta IMN Ibrahim Musa ya ce hukuncin babbar nasara ce a wurin mabiya mazhabar

"Mun yi godiya ga Allah madaukakin sarki da Ya fara nunawa ko kuma tabatar wa da jama'a cewa lallai gaskiya na tare da mu. Domin an tuhumes u da lafi kuma kotu ta wanke su, ta ce ba su da laifi". in ji shi.

Har yanzu dai shugaban 'yan Shi'a a Najeriya, Sheikh Ibrahim El Zakzaky na hannu jami'an tsaro tun bayan arangamar da mabiyansa suka yi da jamian tsaro

Al'amarin da ya yi sanadiyar mutuwar 'yan shi'a fiye da dari uku.

Gwamnatin jihar Kaduna na tuhumar malamin da hannu a kisan wani jami'in soja a lokacin rikicin.

Kisan sojan na cikin tuhumce-tuhumce takwas da gwamnatin ta shigar a gaban kotun a kan malamin da wasu karin mutum uku.