Ficewar Saraki ba ta ba ni mamaki ba — Ndume

Ndume ya ce 'yanzu mun san matsayin Saraki'

Wasu 'yan majalisar dattijan Najeriya na jam'iyyar APC sun ce ba su yi mamakin fitar Sanata Abubakar Bukola Saraki daga jam'iyyar APC din ba.

A ranar Talata ce shugaban majalisar dattijan Najeriya Bukola Saraki ya ce ya fita daga jam'iyyar APC bayan shawarwari da ya yi da wadanda suka kamata.

Sanata Muhammad Ali Ndume, wani dan majalisar dattijai na jam'iyyar APC ya ce bai ji mamakin ficewar Bukola Saraki daga jam'iyyar ba.

"Dama muna tsammani zai tafi saboda haka ba abin mamaki ba ne, kuma ba abin damuwa ba ne."

Ndume ya kara da cewa sun yi maraba da sauya sheka da shugaban majalisar ya yi, domin a cewarsa yanzu sun gane gaskiyar matsayin shi "A da muna kallon sa kamar namu, amma yanzu a bayyane shi ba namu ba ne."

Sai dai Ndume din ya ce jam'iyyar A.P.C dole ne ta damu a duk lokacin da ko da mutum guda ne ya fice daga jam'iyyar.

Ya kuma ce wadanda ke ficewa daga jam'iyyar na daukan wannan mataki ne kasancewar ba su samu wasu bukatu nasu da suka nema ba.

Sai dai Ndume bai fadi matakin da 'yayan majalisar dokokin kasar za su dauka kan shugaban majalisar ba idan sun dawo daga hutu.

A cikin sanarwar da sanata Saraki ya bayar ta ficewa daga jam'iyyar APC, ya ce zai koma jam'iyyar adawa ta PDP domin samun daman bayar da gudumawa domin ci gaban mulkin demokradiyya a Najeriya.

Ko a cikin makon da ya gabata ma 'yan majalisar dokokin Najeriya 52 ne suka sauya sheka daga jam'iyyar ta APC.