Tashe-tashen hankula a Najeriya sun yi kamari - Red Cross

ICRC ta ce ta kula da lafiyar 'yan gidun hijira

Asalin hoton, ICRC

Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross ta bayyana matukar kaduwarta kan halin da mutanen da rikice-rikice suka raba da gidajensu a Najeriya ke ciki.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Laraba kan aikin agajin da ta bayar daga watan Janairu zuwa watan Yunin shekarar 2018, ta koka kan yadda ake samun kwararar 'yan gudun hijira daga Kamaru zuwa Najeriya baya ga wadanda aka tilastawa ficewa daga gidajensu a jihohi irin su Benue da Kaduna da Nasarawa da Filato da kuma Taraba.

A cewar Red Cross, rikice-rikicen kabilanci da wadanda aka yi tsakanin manoma da makiyaya da kuma hare-haren mayakan Boko Haram sun jefa kasar cikin mawuyacin hali na 'yan gudun hijira.

Sanarwar, wadda wata jami'ar Red Cross, Eleojo Esther Akpa, ta sanya wa hannu ta ce kungiyar ta taimakawa mutanen da bala'in ya raba da gidajensu ta bangarori daban-daban.

"Mutum 490,000 daga arewa maso gabas da arewa ta tsakiyar kasar suka samu tallafin kayan abinci, kuma a cikin su mutum mun taimakawa mutum 288,000 da iri da za su yi amfani da shi wajen yin noma", in ji Red Cross.

Kungiyar ta ce, "Kazalika, an tallafawa mutum 180,000 daga arewa maso gabas da arewa ta tsakiya da kuma kudancin kasar da kudin kashewa da na jari domin farfadowa daga matsalolin da suka fada a ciki."

Red Cross ta kara da cewa ma'aikatanta sun bai wa mutane 213,000 da rikice-rikicen suka raba a arewa maso gabas da kudancin kasar damar samun tsaftataccen ruwan sha da kuma kula da lafiyarsu.

Kungiyar ta ce za ta ci gaba da aiki da kungiyoyi masu zaman kansu da hukumomi wurin ganin an inganta rayuwar mutanen da rikice-rikice suka shafa.

Asalin hoton, ICRC

Asalin hoton, ICRC