Abin da ya sa na koma PDP – Tambuwal

Tambuwal Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption Tambuwal ya taba rike mukamin shugaban majalisar wakilan Najeriya a shekarar 2011 zuwa 2015

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya bayyana dalilan komawarsa jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

A wani jawabin da ya yi wa magoya bayansa a gidan gwamnatin jihar Sokoto ranar Laraba, Tambuwal ya ce ya fice ne daga jam'iyyar saboda Shugaba Buhari bai kai ayyukan ci gaba jihar ba.

Har ila yau ya kara da cewa ya dauki matakin ne saboda shugaban bai je jihar ya yi wa mutane jaje ba a lokacin da aka kashe wadansu mutane a jihar.

Hakazalika, gwamnan ya ce gwamnatin Shugaba Buhari ba ta bai wa 'yan jihar mukamai ba.

Gwamnan na jihar Sokoto daya ne daga cikin jigajigan 'yan siyasar da suka fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC gabannin zaben shekarar 2015.

Ya ce matsayinsa na shugaban majalisar wakilai ya fara gwagwarmaya don tabbatar da shugabanci na nagari a kasar.

Sai dai ya ce bayan shekara hudu yanzu "kasar ta fada cikin mawuyacin hali wanda ba a taba ganin irinsa ba tun bayan Yakin Basasar Kasar, inda ake yawan samun rikice-rikice addinin da na kabilanci," in ji shi.

Ya ce ana kuma dora laifin hakan ne ga abokan adawar siyasa.

Gwamnan ya ce ya yi jawabin ne cikin bakin ciki saboda "ban taba tunanin cewa jam'iyyar APC, wadda ta yi alkawurra da dama lokacin da PDP ta tafka kura-kurai, ta kasa dora daga abubuwa masu kyau da ta gada."

"APC ta kasa yin wadansu ayyuka sabbi kuma ta kasa magance matsaloli da suka samu muka fice daga jam'iyyar PDP shekara hudu da suka gabata.

"APC ta mayar da kanta wani wuri na cin hanci da rashawa da magudi da kuma danne tafarkin dimokradiyya."

Jerin sunayen jiga-jigan da suka sauya sheka zuwa yanzu

 • Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki
 • Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal
 • Kakakin jam'iyyar APC Bolaji Abdullahi Ahmed
 • Jakadan Najeriya a Afirka Ta Kudu, Ahmed Ibeto
 • Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom
 • 'Yan majalisar dokoki ta kasa fiye da 50 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP da suka hada da Kwankwaso da Hunkuyi da Melaye da Hamma Misau da Nazif Gamawa da sauran su
 • Bangaren Akida da Restoration a jihar Kaduna wadanda ke rigima da Gwamna Nasir el-Rufa'i
 • Bangaren rAPC na Buba Galadima ya kulla alaka da PDP domin kayar da APC a 2019 - wasu na ganin su ma sun kama hanyar ficewa daga jam'iyyar
 • Sanata Abdul-Azeez Nyako da Dan majalisar Wakilai Rufai Umar daga Adamawa sun koma jam'iyyar ADC
 • Hakeem Baba Ahmed - shugaban ma'aikata a ofishin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki
 • Usman Bawa - mataimaki na musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.