Buhari zai yi hutun kwana 10 a Landan

Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai fara hutun kwana 10 a ranar Juma'a, kamar yadda fadar shugaban kasar ta bayyana.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu, ya wallafa, a shafinsa na Twitter, ya ce, shugaban ya rubuta wa Majalisar Dokokin kasar takardar sanar da ita hakan.

Ya ce shugaban zai yi hutun ne a birnin Landan a kasar Birtaniya. Amma sanarwar ba ta yi magana kan ko shugaban zai ga likitocinsa kamar yadda ya saba idan ya je kasar ba.

Har ila yau ya ce Mataimakin Shugaban Kasar Yemi Osinbajo ne zai jagoranci kasar a matsayin mukaddashin shugaban kasa a lokacin hutun.

Sai dai ba wannan ne karon farko da shugaban ya dauki hutu ba, don ko a farkon shekarar 2017 ya yi hakan.

Labarai masu alaka