Zafi zai dinga kashe mutane cikin sa'a 6 a China a 2070 - Bincike

zafi

Asalin hoton, Getty Images

Wani nazari ya ce nan da karshen karnin da muke ciki wasu yankuna na kasar China da ke cike da mutane a yanzu, za su gagari al'umma zama a dalilin tsananin zafi.

Masu binciken daga wata cibiyar bincike da ke Massachusetts a Amurka, sun ce ana hasashen cewa yankin wanda yanzu ke kunshe da mutane miliyan hudu, zai fi kowanne fama da karuwar zafi a doron kasa.

Binciken ya nuna nan da shekara ta 2070 yanayin zafi a yankin zai iya kashe mutum cikin sa'a shida ko da kuwa a cikin inuwa ce.

Yankin na arewacin China zai zamo mafi hadari a duniya, kuma yana daga cikin yankin da ya fi yawan al'umma a duniya kuma nan ne yankin da aka fi samar da abinci a kasar.

Sabon binciken kimiyyar ya nuna cewa tsannain zafin zai dinga kashe mutane masu cikakkiyar lafiya ma cikin 'yan sa'o'i, kuma zai ta faruwa a yankin wuraren karshen wannan karnin sakamakon sauyin yanayi, sai dai idan an rage amfani da hayaki mai gurbata muhalli," a cewar binciken

Farfesa Elfatih Eltahir na Jami'ar Massachusetts wanda shi ne ya jagoranci binciken ya ce: "Wannan wajen zai zama mafi tsananin zafi a nan gaba.

"Lamarin yana da matukar daga hankali saboda mafi yawan mutane miliyan 400 da suke zaune a yankin manoma ne, kuma bayan wannan ba su da wata damar samun aiki a wani wajen," in ji Farfesan.

Sabon nazarin ya tantance tasirin sauyin yanayi a gwamutsa mai kitsa ta zafi da danshi, wacce ake aunawa da yanayin "jikakken kwan lantarki" (wato "wet bulb" temperature ko WBT a Turance).

Idan yanayin WBT ya kai awo 35 a ma'aunin celsius, iska za ta yi zafi da danshin da jikin dan-Adam ba zai iya iya sanyaya kanshi ba ta hanyar fitar da gumi, sannan hatta mutanen da ke da lafiyar jiki da ke zaune a inuwa za su riga mu gidan gaskiya a cikin sa'a shida.